Kwana Ya Kare: Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Abuja
- Allah ya yi wa tsohon shugaban jam'iyyar PDP reshen Abuja, Alhassan Gwagwa rasuwa ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba, 2024
- An ruwaito cewa jigon PDP ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya a gidansa da ke Gwagwa, ƙaramar hukumar birni AMAC a Abuja
- Manyan jam'an gwamnati da ƴan siyasa daga Nasarawa, Neja da Abuja sun halarci sallar jana'izar marigayin a ranar Litinin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon shugaban babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa watau PDP reshen babban birnin tarayya Abuja, Alhaji Alhassan Gwagwa ya rasu.
Alhaji Alhassan Gwagwa ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da rashin lafiya yana da shekaru 81 a duniya.
Tsohon shugaban PDP a Abuja ya rasu
Wani dan gidan marigayin, Shuaibu Ibrahim Gwagwa ya ce tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya rasu ne da misalin karfe 1:30 na tsakar dare ranar Litinin a Gwagwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa marigayi Alhassan ya riƙe kujerar shugaban jam'iyyar PDP reshen Abuja a tsakanin 2003 zuwa 2013.
An tattaro cewa Sarkin Suleja, Alhaji Awwal Ibrahim, shi ne ya jagoranci jana'izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a jiya Litinin.
Manyan jami'an gwamnati sun halarci janaza
Jana'izar dai ta samu halartar manyan jami'an gwamnati da ƴan siyasa daga birnin tarayya Abuja da jihohin Nasarawa da Neja.
Ya rasu ya bar ‘ya’ya da dama da suka hada da kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Neja, Alhaji Yahaya Alhassan Gwagwa.
Haka nan kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar birni AMAC a Abuja a zaben 2022, Alhaji Sulaiman Alhassan Gwagwa yana ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayin.
Kafin rasuwarsa shi ke riƙe da sarautar Galadiman Gwagwa da ke ƙaramar hukumar AMAC a birnin tarayya, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Matar tsohon hafsan tsaro ya rasu
A wani labarin, an ji cewa matar tsohon hafsan tsaron Najeriya, Admiral Ola Sa'ad Ibrahim ta rasu bayan fama da gajeruwar jinya a birnin Abuja.
Marigayiyar mai suna Aminat Dupe Ibrahim ta rasa ranta a Abuja a daren ranar Talata 5 ga watan Nuwambar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng