"Mutane Sun Jahilci Aikin Ƴan Majalisa," Kakakin Majalisar Dokoki Ya Faɗi Mafita
- Kakakin majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya ce mafi akasarin ƴan Najeriya ba su san menene amfanin majalisa ba
- Tajudeen ya ce akwai bukatar wayar da kai da ilimantar da al'umma kan nauyin da ke kan kowane ɓangare a mulkin demokuraɗiyya
- Ɗan majalisar ya kuma yi kira ga matasa da su shigo a dama da su, su nemi kujeru ba wai na siyasa kaɗai ba domin kawo canji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya ce galibin ƴan Najeriya sun jahilci ayyukan ƴan majalisa a tsarin demokuraɗiyya.
Tajudeen ya ce akwai bukatar wayar da kai da ilimantar da al'ummar ƙasar nan domin su san nauyin da ya rataya a kan ƴan majalisa.
Ya faɗi haka ne a zangon ƙarshe na taron gasar kacici-kacici kan "Majalisa da demokuraɗiyya 2024," a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisa ya magantu kan aikinsu
Kakakin majalisar ya ce wannan taron zai ba matasa damar sanin wasu daga cikin ayyunan majalisar dokoki ta ƙasa.
Tajudeen ya ce:
"Akwai rashin fahimta a tsakanin mutane game da aikin ƴan majalisa, wasu na ganin ƴan siyasa ne kawai ake tarawa su yi ta mahawara, amma abin ya wuce nan."
Majalisa ita ce injin dimokuradiyya, ita ce wurin da ake sauraron koken al'umma kuma nan ne wurin da ake ɗaukar matakai masu muhimmanci a kasa
"Domin dimokuradiyya ta yi aiki yadda ya kamata, dole ne ‘yan kasa su fahimci tsarinta da kuma rawar da kowace ɓangare ke takawa.”
Kakakin majalisa ya ba matasa shawara
Tajudeen ya bukaci matasa su tashi tsaye su nemi kujerun shugabanci ba wai a siyasa kadai ba, a kowane ɓangare domin za su iya kawo sauyi mai ɗorewa.
A cewarsa matasa za su iya taka rawar ganin wajen kawo ci gaba da sauyin da ake buƙata a ƙasar nan, jaridar Punch ta ruwaito.
Majalisa za ta magance yawon yara a gari
A wani rahoton, an ji cewa majalisar dokokin kasar nan ta fara shirin daukar matakin da zai magance yadda iyaye ke kin tura yaransu makaranta.
Matakin ya biyo bayan koken shugaban majalisa, Godswill Akpabio na cewa yara akalla miliyan 20 ba sa zuwa makaranta.
Muhammad Malumfashi, babban Edita a sashen Hausa, Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng