Tsadar Rayuwa: Tinubu ya Karfafi Yan Najeriya, Ya yi Kyakkyawan Albishir

Tsadar Rayuwa: Tinubu ya Karfafi Yan Najeriya, Ya yi Kyakkyawan Albishir

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya da su kara hakuri kan halin wahalar rayuwa da suke ciki a halin yanzu
  • Haka zalika gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce tabbas ana fama da wahalar rayuwa amma sun jajirce a kawo karshen matsalar
  • Shugabannin sun yi magana ne yayin wani taro na musamman da aka shirya domin taya Fasto Tunde Bakare murnar cika shekaru 70

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce sannu a hankali za a magance matsalolin da suka addabi Najeriya.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya wakilci Bola Tinubu yayin taron taya Fasto Tunde Bakare murnar cika shekaru 70.

Shugaba Tinubu
Tinubu ya bukaci yan Najeriya su kara hakuri. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwamnonin jihohi da manyan Najeriya sun halarci taron, ciki har da Malam Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Tinubu zai gabatar da bukatu 2 a taron kasashen musulunci da larabawa a Saudiyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce za a samu sauki a gaba

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa da sannu za a samu sauki a kan halin da ake ciki a tarayyar Najeriya.

Bola Tinubu ya ce idan aka shiga matsala mai sarkakiya ba lallai a samu magani a nan take ko a lokaci daya ba.

"Lallai ana fama da wahalar rayuwa a Najeriya amma akwai tabbacin samun sauki a gaba.
Idan aka shiga matsaloli to ba lallai a fita a kankanin lokaci ba. Ina da tabbas a kan mun ɗauki hanyar fita daga wahalar rayuwa."

- Bola Tinubu

Gwamnan Legas ya bukaci a rika addu'a

A daya bangaren, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce akwai matsalolin tattalin arziki a Najeriya amma suna kan kokarin samar da mafita.

Punch ta wallafa cewa Babajide Sanwo-Olu ya ce suna bukatar addu'ar yan Najeriya wajen fitar da kasar daga wahalar rayuwa da ake fama da ita.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan wasu kalaman Atiku, ya yi zazzafan martani

Gwamnati ta yi raddi ga Atiku Abubakar

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce ya kamata Atiku Abubakar ya koma ya warware rikicin PDP maimakon sukan Tinubu.

Fadar shugaban kasa ta ce Atiku Abubakar yana yi wa Bola Tinubu hassada ne a kan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng