Dangote Ya Cimma Matsaya da 'Yan Kasuwa kan Jigilar Fetur, An Samu Bayanai

Dangote Ya Cimma Matsaya da 'Yan Kasuwa kan Jigilar Fetur, An Samu Bayanai

  • Bayan kwashe dogon lokaci ana kai kawo tsakanin matatar Dangote da ƙungiyar IPMAN, daga ƙarshe dai an cimma matsaya
  • Ƙungiyar dillalan man ta IPMAN ta sanar da cimma yarjejeniya da matatar Dangote domin fara jigilar man fetur kai tsaye
  • Shugaban ƙungiyar wanda ya tabbatar da hakan ya buƙaci mambobin IPMAN da su marawa Dangote baya a samar da ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN) ta cimma yarjejeniya da matatar man Dangote.

Ƙungiyar IPMAN ta ƙulla yarjejeniya da matatar man Dangote domin jigilar man fetur kai tsaye.

IPMAN ta cimma yarjejeniyar da matatar Dangote
Dangote ya cimma yarjejeniya da dillalan fetur Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Shugaban ƙungiyar IPMAN na ƙasa, Abubakar Garima, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai ranar Litinin a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganawa da manema labaran na zuwa ne bayan kammala taron kwamitin gudanarwa na ƙasa na ƙungiyar.

Kara karanta wannan

Jiragen yakin sojojin sama sun soye 'yan ta'addan ISWAP masu yawa a Borno

Kungiyar IPMAN ta cimma yarjejeniya Dangote

Ya ce yarjejeniyar za ta tabbatar da samar da man fetur mai rahusa a duk faɗin ƙasar nan.

"Bayan mun gana da Aliko Dangote da tawagarsa a Legas, muna farin cikin sanar da cewa matatar Dangote ta amince ta ba IPMAN man fetur, AGO, da DPK kai tsaye domin rabawa ga wuraren ajiyarmu da gidajen mai."

- Abubakar Garima

Abubakar Garima ya buƙaci ƴan ƙungiyar IPMAN da su marawa matatar Dangote baya, inda ya bayyana alfanun da ke tattare da hakan ga tattalin arziƙin ƙasar nan.

"Ya kamata ƴan kungiyar IPMAN su dogara da matatar Dangote da matatun man Najeriya wajen samun fetur, domin samar da ƙarin guraben ayyukan yi da kuma tallafawa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu."

- Abubakar Garima

Matatar Dangote ta yi kasuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar man Dangote na shirin fara jigilar man fetur zuwa kasashen ƙetare da suka haɗa da Afirka ta Kudu, Angola da Namibiya.

Kara karanta wannan

Afirka ta Kudu da wasu ƙasashe 7 sun fara shirin sayen futur daga matatar Ɗangote

Masu kula da al'amuran matatar man attajirin ɗan kasuwar mai karfin ganguna 650,000 suna ci gaba da tattaunawa da kasashen domin fitar da mai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng