"Ba a Fahimce Ni ba," Sanata Sani Ya Faɗi Alherin Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya

"Ba a Fahimce Ni ba," Sanata Sani Ya Faɗi Alherin Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya

  • Sanata Sani Musa ya ce ƴan Najeriya sun masa gurguwar fahimta kaan kalaman da ya yi game da cire tallafin man fetur a Najeriya
  • Shugaban kwamitin kudi na majalisar dattawa ya ce cire tallafin zai taimaka wajen kawo ƙarshen cin hanci da rashawa
  • Sani Musa ya ce dama wasu mutane ƙalilan ke cinye makudan kudin tallafin da ya kamata a gina ababen more rayuwa a ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata mai wakiltar Neja ta Gabas, Sani Musa, ya ce ya goyi bayan cire tallafin man fetur ne domin zai tsohe ƙofar cin hanci da rashawa.

Sanatan ya kuma yi ƙarin haske kan ma'anar kalaman da ya yi a makon jiya, inda ya ce cire tallafin mai shi ne abu mafi alheri a Najeriya.

Sani Musa.
Sanata Sani Musa ya ce cire tallafin mai zai kawo karshen cin hanci da rashawa Hoto: Umar Adamu Bako
Asali: Facebook

Sani Musa, shugaban kwamitin kuɗi na majalisar dattawa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kai dauki ga iyalan mutanen da 'yan bindiga suka kashe a jiharsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cire tallafin fetur ya kawo wahala a Najeriya

Tuge tallafin man fetur da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ya jefa ƴan Najeriya cikin kunci da tsadar rayuwa.

Daga lokacin da aka cire tallafin zuwa yau farashin kayayyakin amfanin yau da kullum ya nunnuka, lamarin da ya jefa mutane cikin halin ƙunci.

Dubban ƴan Najeriya sun yi zanga-zangar nuna adawa da manufofin gwamnati mai ci, inda suka nemi a dawo da tallafin amma gwamnati ta dage cewa za a ji daɗi a gaba.

Sanata Sani ya ce matakin zai toshe cin hanci

Da yake karin haske kan lamarin, Sanata Sani ya yarda cewa wahalhalu na karuwa a kasar amma a ganinsa cire tallafin shi ya fi dacewa a yanzu.

Ya ce wasu mutane ƙalilan ne ke amfana da kudin tallafin, wanda ya kamata a yi amfani da su wajen gina ababen more rayuwa a kasar nan.

Kara karanta wannan

"Shi ne mafi alheri" Sanata a Arewa ya fito da manufar cire tallafin mai a Najeriya

"Kalaman da na faɗa cewa cire tallafi shi ne abu mafi alheri ba yana nufin na manta da halin ƙuncin da ake ciki ba, a nufi na an daƙile wasu tsiraru da ke cinye tallafin tsawon shekaru."
"Cire tallafin wani mataki ne na kawar da cin hanci da rashawa da kuma amfani da kudin a bangarorin da suka dace,” inji shi.

An kara rokon Tinubu ya dawo da tallafi

A wani rahoton, an ji cewa wata kungiyar Arewa ta tsakiya ta sake tunkarar shugaban kasa Bola Tinubu kan maganar maido tallafin man fetur da ya cire.

MBF ta ce babu buƙatar dogon nazari domin fahimtar illar da cire tallafin mai ya yi wa tattalin arzikin Najeriya cikin watanni 17.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262