'Yan Bindiga Sun Buɗewa Mutane Wuta a Babban Birnin Jiha, An Rasa Rayuka
- Ƴan bindiga sun yi ajali mutum biyu, sun jikkata wasu a wani hari da suka kai Abeokuta, babban birnin jihar Ogun ranar Litinin
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda, Omolola Odutola ta ce lamrin ya faru ne da tsakar dare misalin ƙarfe 12:30
- Ta ce rundunar ƴan sanda ta fara bincike kan lamarin domin hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Rahotanni sun nuna cewa a yau Litinin, wasu miyagun ƴan bindiga suka budewa mutane wuta a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Ƴan bindigar da ba su wuce su uku ba sun kashe mutane biyu tare da jikkata wasu mutum biyu a mummunan harin.
Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da afkuwar lamarin a wata sanarwa, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na safe a wuraren ajiye motoci na Diamond Dumplings a Abeokuta.
Yadda ƴan bindiga suka kashe mutum 2
A ruwayar Daily Trust, Oduntola ta ce:
"Ƴan bindiga uku ɗauke da makamai a cikin wata mota Hilux ne suka farmaki wasu mutane a motar Marsandi suka nemi su fito su ba su makullin motar.
"A ƙarshe dai maharan suka buɗe wuta, suka harbi wani mai suna Ola da Shobanke Oluwatimileyin da wasu mutum biyu."
"DPO na caji ofis din Ibara ya isa wurin da wuri bayan samun kiran gaggawa kuma sai da ya tabbatar da tsaro a yankin kafin ɗaukar waɗanda maharan suka harba zuwa asibiti."
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
Kakakin ƴan sandan ta ƙara da cewa daga isa asibiti, likitoci suka tabbatar da mutuwar mutum biyu yayin da sauran kuma aka kwantar da su don masu magani.
Odutola ta ce rundunar ƴan sanda ta fara gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya jawo kisan mutanen da kuma ɗaukar mataki kan miyagun.
An kama jagoran ƴan bindiga a Ogun
A wani rahoton, mun kawo maku cewa dakarun Amotekun a Kudu maso Yamma sun kama wani dan bindiga da ake zargi da kisan wasu mata.
Ana zargin cewa Ogunnaike Philip ya yi wa wasu yan mata kisan gilla ne kuma ya wulakanta gawarsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng