Taoreed Lagbaja: An Fadi Lokacin Jana'izar Tsohon Shugaban Sojojin Najeriya

Taoreed Lagbaja: An Fadi Lokacin Jana'izar Tsohon Shugaban Sojojin Najeriya

  • An fara batun jana'izar tsohon shugaban hafsan sojojin ƙasan Najeriya (COAS), marigayi Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja
  • Babban yayan marigayin ya bayyana cewa za a binne shi a ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamban 2024 a birnin tarayya Abuja
  • Ya ba da tabbacin cewa za a yi wa marigayin jana'izar da ta dace da shi bayan rasuwarsa a ranar, 5 ga watan Nuwamba a birnin Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - An fara maganar binne tsohon hafsan sojojin ƙasan Najeriya (COAS), Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja.

Rahotanni sun nuna cewa in dai ba wani sauyi aka samu ba, za a yi jana'izar marigayi Lagbaja ne a ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamban 2024 a birnin tarayya Abuja.

Za a binne Taoreed Lagbaja
Za a yi jana'izar Taoreed Lagbaja ranar Juma'a Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Za a yi jana'izar Taoreed Lagbaja

Babban yayansa, Moshood Lagbaja, ne ya bayyana hakan a birnin Osogbo na jihar Osun, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Na yi nadamar nema masa fom a NDA': Baffan marigayi Lagbaja ya magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Moshood Lagbaja ya yi batun jana'izar marigayin ne yayin wata ziyarar ta'aziyya da ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na makarantar St Charles Grammar School Osogbo (SCOBA) ta kai musu

Ya bayyana cewa sojoji ba za su ba da gawar Taoreed Lagbaja ga iyalansa ba, amma ya ba su tabbacin za a yi masa jana’izar da ta dace a Abuja ranar Juma’a.

Tawagar ta gabatar da takardar ta’aziyya mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na duniya, Tade Adekunle da kuma babban sakatarenta, Leye Odetoyinbo, ga iyalan marigayin, rahoton Leadership ya tabbatar.

Da yake jawabi a madadin ƙungiyar SCOBA, jagoran tawagar, wanda kuma shi ne mataimakin shugaba na ɗaya, Injiniya Adesina Salami, ya bayyana marigayi Lagbaja a matsayin mutum na musamman.

Ya ce marigayin jajirtaccen jarumin soja ne wanda ya yi wa ƙasarsa hidima bisa sadaukarwa.

Gwamnoni sun yi ta'aziyyar Janar Lagbaja

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta yi alhinin rasuwar hafsan sojojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƙasa ya faɗi abin da matarsa ta yi lokacin da yake gidan yari

Gwamnonin jihohi 19 na Arewacin Najeriya ƙarƙashin ƙungiyarsu watau NSGF, sun aika sakon ta'aziyyar rasuwar Lagbaja ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng