Saboda Wata Matsala, Gwamna Zai Biya Ma'aikata Albashi 2 a Watan Disamba

Saboda Wata Matsala, Gwamna Zai Biya Ma'aikata Albashi 2 a Watan Disamba

  • Gwamna Umo Eno ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta biya ma’aikatan Akwa Ibom albashi biyu a cikin Disamba
  • Wannan albashi na “Eno-Mber” a cewar gwamnan zai taimaka wajen samar da farin ciki ga ma'aikata a lokutan bikin Kirsimeti
  • Rahotonni sun nuna cewa gwamnan ya dauki matakin ne bayan jinkirin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Akwa Ibom - Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya tabbatar da cewa za a biya ma’aikatan jihar albashi biyu a watan Disambar 2024.

Gwamna Eno ya bayyana cewa biyan albashin sau biyu, mai taken “Eno-Mber” ya zama wajibi domin sanya ma'aikata farin ciki a bikin Kirsimeti.

Gwamna Umo Eno ya yi magana kan biyan ma'aikatan Akwa Ibom albashi biyu
Gwamnan Akwa Ibom zai biya ma'aika albashi biyu a watan Disamba. Hoto: @_PastorUmoEno
Asali: Twitter

Gwamna Eno zai biya albashi biyu a Disamba

Jaridar Leadership ta gano cewa biyan albashin biyu (albashin wata na 13) ya biyo bayan jinkirin fara biyan mafi ƙarancin albashi na N80,000 a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan ayyana ilimi kyauta, gwamna a Arewa ya kawo sabon tsari a manyan makarantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa kwamitin da aka kafa kan sabon albashin ya gaza mika rahoto a cikin lokacin da aka tsara masa, wanda ya kawo jinkirin.

Saboda ya kwantar da hankalin ma’aikatan jihar, Gwamna Eno ya sanar da biyan albashi biyu a Cocin Eternity Mission International, Uyo lokacin da ya je bauta.

Gwamnan A/Ibom zai ba ma'aikata kyautar N1.1bn

Gwamna Eno ya gargadi masu ƙoƙarin kawo cikas ga kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin gwamnatin jihar da ƙungiyoyin ƙwadago.

Ya yi alkawarin ba da kyautar Naira biliyan 1.1 ga ma’aikatan gwamnati da kuma biyan albashi da fansho da giratuti a kan lokaci, a cewar shafin gwamnatin Akwa Ibom.

Gwamnan ya sake fitar da kuɗi don tabbatar da biyan tallafin albashi ga ma’aikatan jihar tsawon watanni uku, domin rage radadin janye tallafin fetur.

Gwamnan Akwa Ibom zai kara aure?

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Akwa Ibom Umo Eno ya yi martani ga rade radin da ke yawo na cewa zai kara aure bayan mutuwar matarsa.

Kara karanta wannan

Ana murna, malaman makaranta sun fara karbar sabon albashin N70,000 a jihar Arewa

Gwamna Eno ya ce ba shi da niyyar kara aure a yanzu saboda bai kammala tara kudin sadaki ba tukunna, inda ya ce zai fi mayar da hankali wajen ci gaban jiharsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.