Yahaya Bello: Matasan APC Sun ba Tsohon Gwamna Shawara kan Takaddamarsa da EFCC
- Wata ƙungiyar matasa mai suna APC Youth Vanguard ta nuna damuwarta kan yadda Yahaya Bello ke ci gaba da ƙin kai kansa kotu
- Ƙungiyar ta nuna takaicin cewa rashin amsa sammacin kotu da tsohon gwamnan Kogi yake yi abin kunya ne ga jam'iyyar APC
- Ta buƙaci Yahaya Bello da ya kai kansa a gaban kotu domin ya fuskanci tuhume-tuhumen da hukumar EFCC ke yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wata ƙungiya mai suna APC Youth Vanguard ta buƙaci tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da ya gurfana a gaban kotu.
Yahaya Bello dai na fuskantar tuhume-tuhume akalla 19 kan badakalar kuɗi har Naira biliyan 80.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, jagoran ƙungiyar Rasheed Sanusi, ya ce rashin bayyanar Yahaya Bello a gaban kotu abin kunya ne ga jam’iyyar APC, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya koka da cewa wasu har sun fara fassara rashin amsa sammacin kotu da tsohon gwamnan yake yi a matsayin samun kariya daga fadar shugaban ƙasa saboda rawar da ya taka wajen yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima.
Wace shawara matasan APC suka ba Yahaya Bello?
Rasheed Sanusi ya bayyana cewa ya kamata Yahaya Bello ya yi koyi da sauran tsofaffin gwamnoni waɗanda suka tsaya aka gurfanar da su a gaban kotu kan zarge-zargen da ake yi musu.
"A makon da ya gabata aka kama tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, aka kuma bayar da belinsa. Haka kuma, gwamnan jihar Edo mai barin gado, Godwin Obaseki ya bayyana a shirye ya ke ya amsa gayyatar EFCC, idan an gayyace shi."
"To, meyasa Yahaya Bello ke ƙin amsa sammacin kotu? Su wanene a fadar shugaban ƙasa da ake zargin suna ba Yahaya Bello kariya?"
"Wannan abin da ke faruwa abin kunya ne ga jam’iyyar mu da fadar shugaban ƙasa da ma ƙasa baki ɗaya."
"Abin kunya ne babba. Muna roƙon Yahaya Bello da ya fito bisa radin kansa domin gurfanar da shi a gaban kotu ko kuma a tilasta masa yin hakan ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin hukumomi. Ya isa haka!"
- Rasheed Sanusi
Yahaya Bello ya roƙi Tinubu kan EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jigar Kogi, Yahaya Bello ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani a rikicinsa da hukumar yaƙi da rashawa watau EFCC.
Ofishin yaɗa labaɗai na tsohon gwamnan ne ya yi wannan kira a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng