Yadda Aka Yi Rubdugu ga Sheikh Idris Dutsen Tanshi kan Fatawar Daukar Hoto

Yadda Aka Yi Rubdugu ga Sheikh Idris Dutsen Tanshi kan Fatawar Daukar Hoto

  • A makon da ya wuce malamin addinin Musulunci, Dr Idris Abdulaziz ya yi magana a kan haramcin daukar hoto a shari'a
  • Biyo bayan zazzafar huduba da malamin ya yi a garin Bauchi, wasu malamai a fadin Najeriya sun yi masa raddi kan mas'alar
  • Shugaban malaman Izala, Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya ce abin mamaki ne yadda malamin ke haramta hoto amma yake fitowa bidiyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - A makon da ya wuce Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya yi huduba mai zafi a kan hukuncin daukar hoto a Musulunci.

Dutsen tanshi
Malamai sun yi raddi ga Dr Idris Dutsen Tanshi kan daukar hoto. Hoto: Dutsen Tanshi Majlis Bauchi
Asali: Facebook

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta musamman ganin ana daukar Dr Idris a bidiyo.

Shugaban malaman Izala, Dr Jalo Jalingo ya wallafa a Facebook cewa shari'a ba ta haramta ɗaukar hoto da bidiyo na zamani ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar Dr. Ibrahim Jalo kan daukar hoto

Dr Jalo Jalingo ya bayyana cewa sun yi bincike kuma sun fahimci cewa daukar hoto na zamani yana da hukunci kamar na amfani da madubi ne a shari'a.

Malamin ya kara da cewa duk da cewa akwai wasu daga cikin malamai da suka haramta ɗaukar hoto amma kuma sun haramta bidiyo ma gaba daya.

"Amma abin da nake yawan mamakinsa shi ne fahimtar wanda yake haramta hoto sannan kuma ya halatta bidiyo.
Tabbas wannan mutum ina mamakin irin yadda wannan fahimtar tasa ta kasance haka."

- Dr Ibrahim Jalo Jalingo

Maganar Aliyu Muh'd Sani kan hoto

Dr Aliyu Muhammad Sani ya wallafa a Facebook cewa ba abin mamaki ba ne a samu wanda ya haramta ɗaukar hoto kuma ya halasta bidiyo.

Malamin ya ce hakan zai iya yiwuwa idan aka lura da yadda aka samu sabani a kan matsalolin, abin da ba a so kawai shi ne sukar juna.

Kara karanta wannan

'Babu wanda ya isa': Ministan Tinubu ya lashi takobin rusa gidajen mutane a Abuja

"Mai laifi a mas'alolin Ijtihadi shi ne wanda ya zargi abokan sabaninsa, ya zage su, ya kaurace musu. Saboda ya zama mai raba kan al'umma."

- Dr Aliyu Muhammad Sani

Dutsen Tanshi ya dura kan gwamna

A wani rahoton, kun ji cewa Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya dawo kan Gwamnan Bala Mohammed na jihar Bauchi kan take hakkin al'umma.

Shehin malamin ya caccaki gwamna Bala Muhammad kan tsoma baki a lamarin yaran da aka tsare na tsawon watanni kuma aka kai su kotu a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng