Sojojin Sama Sun Tura 'Yan Bindiga zuwa Barzahu a Jihar Katsina
- Dakarun sojojin sama na Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga a Katsina a wani hari da suka kai a maɓoyarsu
- Gwarazan sojojin sun hallaka ƴan bindiga 15 a harin wanda suka kai a ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina
- Hare-haren waɗanda aka kai ta jiragen sama sun kuma yi sanadiyyar raunata ƴan bindiga masu yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Dakarun sojojin sama na Operation FANSAN YAMMA a ƙarƙashin Operation FARAUTAR MUJIYA na yankin Arewa maso Yamma, sun hallaka ƴan bindiga 15 a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan bindigan ne a wani harin sama da suka kai a ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Majiyoyin sun shaidawa Zagazola Makama cewa an kai hare-haren ne ta jiragen yaƙi a ranar, 10 ga watan Nuwamba, 2024, a kan maboyar ƴan bindiga da ke Arewa maso Yammacin ƙauyen Tsaskiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka murƙushe ƴan bindiga
Majiyar ta bayyana cewa jiragen NAF sun ƙaddamar da hari kan maɓoyar ƴan bindigan inda suka samu nasarar saukar mata da bama-bamai waɗanda suka hallaka ƴan bindiga masu yawa.
Harin sojojin saman ya kuma yi sanadiyyar jikkata ƴan bindiga masu yawa waɗanda suka samu raunuka daban-daban.
Majiyar ta ce harin na sama wani ɓangare ne na Operation Fansa Yamma, wanda ke da nufin tarwatsa sansanonin masu aikata laifuka na Shamo da Shafi’u.
"Harin wanda aka kai da misalin ƙarfe 1:00 na dare, ya yi sanadiyyar kashe ƴan bindiga 15, yayin da wasu da dama aka kai su wani shagon sayar da magunguna da ke Tsaskiya, mallakar wani mai suna Jankare, domin neman magani."
- Wata majiya
Sojojin sama sun hallaka ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun hallaka ƴan ta'adda masu yawa a wasu dazuzzukan da ke tsakanin jihohin Zamfara da Kebbi.
Rahotanni su bayyana cewa ƴan ta’addan, waɗanda wasu daga cikinsu ƴan ƙungiyar Lakurawa ne, an kashe su ne a wani wuri da ake kira Sangeko a Zamfara, kusa da kan iyaka da jihar Kebbi.
Asali: Legit.ng