Amnesty Int'l Ta Caccaki Gwamna bisa Zargin Jikkata Yar Gwagwarmaya

Amnesty Int'l Ta Caccaki Gwamna bisa Zargin Jikkata Yar Gwagwarmaya

  • Kungiyar Amnesty International ta zargi gwamnatin Sakkwato da kokarin dakile gwagwarmaya a fadin jihar
  • Wannan na zuwa bayan wasu mutane sun dauki yar gwagwarmaya, Hamdiyya Sidi tare da yi mata dukan kawo wuka
  • Hamdiyya Sidi ta saki bidiyo ta na tuhumar yadda gwamna Ahmed Aliyu ya bar yan ta'adda na cin zarafinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Kungiyar Amnesty Int'l da ke rajin kare hakkin bil'adama a duniya ta zargi gwamnatin Sakkwato da jikkata wata matashiya, Hamdiyya Sidi.

Matashiyar ta tsokane idanun mahukuntan Sakkwato bayan ta fitar da wani bidiyo da ke kalubalantar gwamna Ahmed Aliyu na barin mutanen kauyukan da ake kai wa hari cikin mugun hali.

Hamdiyya
Amnesty Int'l ta zargi gwamnatin Sakkwato da cin zarafin matashiya Hoto: Hamdiyya Sidi
Asali: Facebook

A sakon Amnesty Int'l a shafin Facebook, ta yi tir da yadda gwamnatin ta sa aka damke Hamdiyya tare da yi ma ta dukan kawo wuka.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun gano hanyar daukar matasa cikin sauki, ta'addanci zai ƙaru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin da Hamdiyya Sidi ke ciki

Wani mai amfani da shafin Facebook, ya wallafa cewa Hamdiyya Sidi na kwance rai a hannun Allah bayan ta sha duka a hannun wasu mutane. Amnesty Int'l ta zargi wasu jami'ai da daukar Hamdiyya da karfin tuwo a cikin keke Napep, sannan su ka jikkata ta.

Amnesty ta yi tir da gwamnatin Sakkwato

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Int'l ta ce ba dai-dai ba ne gwamnatin Sakkwato ta nemi rufe bakin jama'a da ke kuka da mugun halin da su ke ciki.

Kungiyar na ganin gwamnati ta yi amfani da cin zarafin Hamdiyya Sidi domin tsorata duk wadanda ke shirin fito da fito da rashin adalci a jihar.

Amnesty ta aika sako ga gwamnati Amnesty ta aika sako ga gwamnati

A baya mun ruwaito cewa kungiyar Amnesty Int'l ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta daina shari'a da kananan yara bisa zargin kokarin kifar da gwamnatin.

Kara karanta wannan

'Ka hana Wike, gwamnoni ba alkalai motoci da gidaje,' SERAP ta fadawa Tinubu

Kafin a sake yaran, sun shafe akalla kwanaki sama da 90 a hannun jami'an tsaro inda aka garkame su bisa tuhumar adawa da manufofin gwamnati bayan sun fito zanga zangar adawa da yunwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.