'Babu Wanda Ya Isa': Ministan Tinubu Ya Lashi Takobin Rusa Gidajen Mutane a Abuja

'Babu Wanda Ya Isa': Ministan Tinubu Ya Lashi Takobin Rusa Gidajen Mutane a Abuja

  • Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ce babu wani irin zanga-zanga da zai dakatar da shi daga aikin tsabtace Abuja
  • Deji Adeyanju ya jagoranci zanga-zangar adawa da aikin Wike, inda ya bayyana cewa an lalata tarin gidaje da dukiyoyi
  • Sai dai Wike ya tabbatar wa mazauna Ruga cewa ba zai daina rusau ba, yana mai cewa wurin yana da hatsari ga tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya jaddada cewa babu zanga-zangar da za ta dakatar da shirin tsabtace Abuja.

Biyo bayan umarnin ministan, jami’an ma'aikatar Abuja sun rushe wani matsuguni na Ruga da ke kan titin filin jirgin sama a Lugbe, lamarin da ya jawo zanga-zanga.

Nyesom Wike ya yi magana kan zanga zangar da ake yi a Abuja bayan rusau da ya yi
Nyesom Wike, ya ce babu zanga-zangar da za ta hana aikin tsabtace Abuja. Hoto
Asali: Facebook

Zanga-zanga ta barke kan aikin Wike a Abuja

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Deji Adeyanju, wani mai rajin kare hakkin bil'adama, ya jagoranci masu zanga-zanga kan rusa gine-ginen.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi rubdugu ga Sheikh Idris Dutsen Tanshi kan fatawar daukar hoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fitaccen lauyan ya yi korafi kan yadda aka rusa gidajen jama'a, inda ya bayyana cewa an lalata gidaje da dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Adeyanju ya bayyana damuwa cewa an jefa mazauna Ruga cikin mawuyacin hali, yana mai rokon Shugaba Bola Tinubu da ya magance lamarin.

Sai dai Wike ya kai ziyara wurin da aka yi rusau ranar Lahadi, tare da manyan jami’an tsaro, yana mai cewa ya zo domin ganewa idonsa yanayin da ake ciki, inji The Nation.

Nyesom Wike ya lashi takobin yin rusau

Wike ya tabbatar wa mazauna wurin cewa babu ja da baya kan wannan matakin tsabtace Abuja, yana mai cewa wurin na da hadari ga tsaro, musamman ga titin jirgi.

Ministan ya bayyana cewa babu gwamnatin da za ta bar mutane suna zama a wurin da aka samar da shi ba bisa ka’ida ba, musamman wanda ke barazana ga jama’a.

Kara karanta wannan

Sanata ya ga halin da talakawa ke ciki, ya nemi mafita daga shugaba Tinubu

Ya bayyana cewa babu wata irin barazana ko zanga-zanga da za ta iya dakatar da wannan aikin na rusa gidaje ko matsugunnan da aka gina su ba bisa ka'ida ba.

Wike ya nemi mazauna wurin su kawo wakilai guda biyar domin tattaunawa tare da jami’an ma'aikatar FCTA kan tallafin da gwamnati za ta iya ba su.

Wike ya rusa gidaje 100 a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar masu gine-gine ta HBAN ta zargi ministan Abuja, Nyesom Wike da rushe gidaje sama da 100 ba bisa ka’ida ba a Sabon Lugbe.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa rushe-rushen Wike ya raba daruruwan mutane da gidajensu tare da jawo asarar kudaden da ba su yi kasa da N200bn ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.