Mafi Karancin Albashi: NLC Ta Sanar da Lokacin Fara Yajin Aiki

Mafi Karancin Albashi: NLC Ta Sanar da Lokacin Fara Yajin Aiki

  • Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta nuna takaicinta kan yadda wasu jihohi suka kasa fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi
  • NLC ta nuna cewa jinkirin da gwamnonin ke yi na fara biyan ma'aikata sabon albashin, rashin mutunta doka ne
  • Ƙungiyar ta umarci mambobinta a jihohin da ba a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ba, su fara yajin aiki daga Disamban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi magana kan rashin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi a wasu jihohin ƙasar nan.

Ƙungiyar NLC ta nuna takaicinta kan yadda wasu jihohin suke yin tafiyar hawainiya wajen aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin N70,000 ga ma'aikata.

NLC za ta fara yajin aiki
NLC za ta yi yaji aiki kan mafi karancin albashi Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin sanarwar bayan taron NLC na majalisar zartaswa (NEC) wacce ƙungiyar ta sanya a shafinta na nlcng.org

Kara karanta wannan

Lakurawa: Dakarun sojojin sama sun sheke 'yan ta'adda masu tarin yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane umarni NLC ta ba da?

Ƙungiyar ta umarci mambobinta a jihohin da har yanzu ba su fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ba, su fara yajin aikin sai baba-ta-gani, daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024.

"NEC ta lura da matuƙar takaici bisa jinkiri da ƙin wasu gwamnonin jihohi na aiwatar da dokar mafi ƙarancin albashi ta ƙasa na 2024."
"Wannan cin amana da wasu gwamnoni da jami’an gwamnati ke yi a faɗin ƙasar yi wa doka karan tsaye ne, yayin da ake ci gaba da hana ma’aikata albashin da ya dace duk da taɓarɓarewar tattalin arziƙi."
"Wannan rashin mutunta doka ne da kuma rayukan miliyoyin ma’aikatan Najeriya, waɗanda shugabannin da aka rantsar domin su kare su, ke gasa musu aya a tafin hannunsu."
"Don haka, an umarci duk ƙungiyoyin NLC a jihohin da ba a aiwatar da mafi ƙarancin albashi na ƙasa ba zuwa ranar ƙarshe ta watan Nuwamba 2024, da su fara yajin aiki daga ranar, 1 ga watan Disamba."

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta fadi abin da ta sani kan taron addu'a saboda tsadar rayuwa

- Joe Ajaero

Gwamna ya amince da sabon albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Gwamna Seyi Makinde ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin N80,000 wanda za a riƙa biyan ma’aikatan jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng