Ba a Gama Shari'ar Sarautar Kano ba, Sanusi II Ya Shawarci Alkalai, Ya Tuna Musu Allah

Ba a Gama Shari'ar Sarautar Kano ba, Sanusi II Ya Shawarci Alkalai, Ya Tuna Musu Allah

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magana kan halayen wasu daga cikin alkalai da ke hukuncin zalunci
  • Sarki Sanusi II ya shawarci alkalan da su tabbatar da yin adalci a dukan hukunce-hukunce da za su yi ba tare da wariya ba
  • Basaraken ya tuna musu ranar gobe inda ya ce idan ba su yi adalci a duniya ba wa zai tsaya musu a wancan rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Sarki Muhammadu Sanusi II ya shawarci alkalai a Najeriya kan hukuncin adalci.

Basaraken ya ce bai kamata alkalai suna hukunci da zai fifita yan uwa da abokansu ba ko ta wane hali.

Kara karanta wannan

'Ku tsaya gida, ku bar fita kasar waje,' Tinubu ya aika sako ga matasa masu digiri

Sarki Sanusi II ya ba alkalai shawara
Sarki Muhammadu Sanusi II ya shawarci alkalai kan hukuncin adalci a kotu. Hoto: @masarautarkano.
Asali: Facebook

Sanusi II ya ba alkalai shawara kan hukunce-hukunce

Sarki Sanusi II ya fadi haka ne a Lagos yayin karrama Mai Shari'a, Habeed Abiru zuwa Kotun Koli, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bai kamata alkalan su rika hukunci da gayya wanda zai juya su daga gudanar da adalci ba.

Sanusi II yana magana ne musamman ga alkalan Kotun Koli da ke Najeriya wadanda su ne karshe a matakin alkalanci a kasar, TheCable ta ruwaito.

Sanusi II ya yiwa wa'azi kan ranar gobe

"Kada ku zama masu goyon bayan wadanda suka yi laifi ko suka ci amanar kansu."
"Yin hakan kuskure ne saboda Allah bai son masu aikata laifuffuka a doron kasa."
"Idan abokai ko mukarraban gwamnati suka zo muku, ku ka yi hukunci domin faranta musu rai, ku tambayi kanku a ranar gobe waye zai tsaya muku."

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da Tinubu ya isa birnin Riyadh, zai halarci manyan tarurruka 2

- Sarki Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya magantu kan zanga-zanga a Najeriya

A baya, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gana da yaran da Bola Tinubu ya yi wa afuwa kan shiga zanga zangar tsadar rayuwa.

Muhammadu Sanusi II ya buƙaci jami'an tsaro su canja salon kama masu laifi idan aka samu tarzoma ko rikici a tsakanin al'umma.

Sarkin ya kuma yabawa shugaba Bola Tinubu da gwamna Abba Kabir Yusuf kan ganin yaran sun samu yanci bayan kulle su da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.