Ana Masa Dawo Dawo Karo na 2, Jonathan Ya Yi Magana kan Nasarar Trump
- Tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya taya sabon shugaban Amurka, Donald Trump murna
- Jonathan ya ce tabbas Amurkawa sun tabbatar da amincewarsu ga Trump wanda ake sa ran zai kawo zaman lafiya a duniya
- Wannan na zuwa ne yayin da wasu ke kiran dawo-dawo ga Jonathan musamman bayan Trump ya sake nasara a karo na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dakta Goodluck Jonathan ya yi magana kan zaben Amurka.
Jonathan ya taya sabon shugaban kasar, Donald Trump murna kan nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar.
Jonathan ya fadi tasirin nasarar Trump a duniya
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a yau Lahadi 10 ga watan Nuwambar 2024 a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jonathan ya ce wannan nasara ta Donald Trump ya nuna yadda Amurkawa suka aminta da shi da kuma tsare-tsarenda tun a baya.
Ya ce yana da tabbacin nasarar ba iya Amurkawa za ta amfana ba har ma da zaman lafiyar duniya baki daya duba da yadda ya dauko tsare-tsarensa tun farko.
Jonathan ya taya Donald Trump murnar lashe zabe
"Ina taya ka murna samun nasara da ka yi a matsayin shugaban kasar Amurka na 47 bayan kammala zabe a kwanakin nan."
"Wannan nasara taka ta nuna yadda Amurkawa suka aminta da dukan tsare-tsaren da shirya musu."
"Ina da tabbacin nasarar ba iya inganta mafarkin Amurkawa za ta yi ba, har ma da kawo zaman lafiya da cigaba a duniya."
- Goodluck Jonathan
Jonathan ya fadi halin da ya shiga a 2015
Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tuno lokacin da ya fadi zaben da aka gudanar a 2015 a hannun Muhammadu Buhari.
Jonathan ya bayyana irin mummunan yanayi da ya shiga kan faduwa zaben, ya ce ba abu ba ne mai sauki a rayuwa a rasa mulki.
Tsohon shugaban kasar ya ce ba zai taba mantawa da marigayi Raymond Dokpesi ba kan yadda ya tsaya tare da shi a wancan lokaci.
Asali: Legit.ng