Gwamna Ya Yi Magana bayan Sabuwar Kungiyar Yan Bindiga Ta Kashe Mutum 15

Gwamna Ya Yi Magana bayan Sabuwar Kungiyar Yan Bindiga Ta Kashe Mutum 15

  • Gwamna Nasir Idris ya miƙa sakon ta'aziyya ga sarkin Argungu da mutanen garin Mera bayan harin ƴan bindiga
  • Gwamnan ya buƙaci iyalan waɗanda suka rasa rayukansu su ɗauki lamarin a matsayin kaddara daga Allah su yi haƙuri
  • Nasir Idris Kauran Gwandu ya ce gwamnati na aiki ba dare ba rana tare da haɗin guiwar jami'an tsaro don kawar da miyagun laifuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ya miƙa sakon ta'aziyya ga al'ummar kauyen Mera da ke ƙaramar hukumar Augie a jihar Kebbi.

Gwamnan ya jajantawa mutanen garin sakamakon mummunan harin ƴan bindiga, wanda ake zargin sabuwar kungiyar ta'addanci ta Lakurawa ce ta kai harin.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kai dauki ga iyalan mutanen da 'yan bindiga suka kashe a jiharsa

Gwamna Nasir Idris.
Gwamnan Kebbi ya yi ta'aziyyar mutuwar mutum 15 a harin da ƴan bindiga suka kai garin Mera Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Asali: Twitter

Channels tv ta ce Gwamna Idris ya yi ta'aziyyar ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa, Ahmed Idris ya fitar ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Nasir ya yi ta'aziyya ga sarkin Argungu

Gwamnan ya bayyana harin wanda ya lakume rayukan mutum 15 a matsayin "mummuna kuma abin takaici."

"A madadin gwamnatin jihar Kebbi muna mika sakon ta’aziyyarmu ga mai martaba Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu-Mera, da kuma al’ummar garin Mera.
"Muna addu'ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu kuma muna rokon iyalansu da sauran ƴan uwa su rungumi kaddara, su yi hakuri da abin da ya faru."

- Nasir Idris.

Wane matakin gwamnati Kebbi ta ɗauka?

Gwamnan ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnati na daukar dukkan matakan da suka dace tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya.

Nasir Idris ya kuma buƙaci ɗaukacin al'umma su ci gaba da bai wa jami'an tsaro haɗin kai da bayanan sirri domin taimaka masu a yaƙin da suke da ƴan ta'adda.

Kara karanta wannan

Bayan ayyana ilimi kyauta, gwamna a Arewa ya kawo sabon tsari a manyan makarantu

Wannan dai na zuwa ne bayan wata arangama da aka yi tsakanin mazauna garin Mera da mayakan Lakurawa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 15 ranar Juma'a.

Ƴan ta'adda sun kara shigowa Najeriya

A wani rahoton, an ji cewa rundunar sojojin kasar nan ta tabbatar da shigowar sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda daga kasashen Mali da jamhuriyyar Nijar.

Sanarwar da daraktan yada labaran rundunar, Edward Buba ta fitar ta ce yan ta’addan sun yi sansani a Kebbi da Sakkwato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262