'Na Yi Nadamar Nema Masa Fom a NDA': Baffan Marigayi Lagbaja Ya Magantu
- An zargi mutuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja kan rigimar filaye da ake yi a jihar Osun
- Baffan marigayin mai suna Tajudden Lagbaja ya ce ya yi nadamar nema masa fom na NDA a shekarun baya
- Hakan na zuwa ne bayan rasuwar hafsan sojojin Najeriya a jihar Legas bayan fama da jinya wanda har an nada mukaddashinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Baffan marigayi hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja ya yi magana bayan rasuwar sojan.
Tajudden Lagbaja ya ce ya yi nadamar siyawa marigayi Lagbaja fom na soja a makarantar NDA da ke Kaduna.
Zargin da ake yi kan mutuwar Lagbaja
The Nation ta ce Tajudden ya ce ya yi nadamar ne saboda bai san rayuwar Lagbaja za ta kare da wuri ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran yan uwan marigayin suna zargin an kashe shi ne saboda rigimar da ake yi kan filaye a Ilobu a jihar Osun.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu matsala ne kan rigimar filaye a Ilobu da ke karamar hukumar Irepodun.
An samu matsala ne lokacin da hukumar sojoji a 2023 ta shirya gina asibiti a yankin.
Tajudden wanda shi ne kanin mahaifin Lagbaja ya ce shi ya nemowa marigayin fom a NDA.
Baffan marigayi Lagbaja ya magantu kan mutuwar
"Mun godewa Ubangiji da yadda ya jarrabe mu, duk da mun sani duk mai rai mamaci ne."
"Lokacin da na karbo masa fom a NDA da na san zai mutu kafin ni da ban nema masa ba, na yi nadama, amma haka ƙaddara ta nuna."
"Ni ya kamata mutuwa ta dauka ba Lagbaja ba, mun yi rashin ɗa saboda na dauke shi kaman ni na haife shi, ya gina madatsun ruwa a gidan mahaifinsa da kuma sauran wurare a yankin."
- Tajudden Lagbaja
Lagbaja: Gwamna Ademola ya ba hutu a Osun
Kun ji cewa Gwamnatin jihar Osun ta ayyana kwanaki uku domin zaman makoki bayan rasuwar shugaban sojojin kasan Najeriya.
Laftanal Janar Taoreed Lagbaja wanda dan asalin jihar Osun ne ya rasu bayan fama da jinya da ya yi yana dan shekaru 56 a duniya.
A ranar Laraba, 6 ga watan Nuwambar 2024 shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da rasuwar shugaban sojojin.
Asali: Legit.ng