Bayan Shekara da Shekaru Ana Fama, Tinubu Ya Karawa Ministoci 16 Matsayi a Gwamnati

Bayan Shekara da Shekaru Ana Fama, Tinubu Ya Karawa Ministoci 16 Matsayi a Gwamnati

  • Shugaban kasa ya yi na’am da shawarar da aka kawo na ba kananan ministoci cikakken iko a ofis
  • A gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, karamin minista zai yi aiki tamkar duk wani babban minista a doka
  • Yanzu akwai kananun ministoci a majalisar FEC da ta kunshi mutane 48 a gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a ba kananan ministoci cikakken matsayi a gwamnatin tarayya.

An fahimci wannan cigaba ya na zuwa ne shekara da shekaru bayan an fara yunkurin kananan ministoci a gwamnatin Najeriya.

Sababbin ministoci
Bola Tinubu lokacin rantsar da sababbin ministoci a Najeriya Hoto: @KashimSM
Asali: Twitter

Kananan ministoci sun samu karin karfi

A ranar Juma’a The Cable ta kawo labari cewa kananan ministoci sun samu cikakken iko kamar sauran manyan ministoci.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, an bayyana dalilin Tinubu na sakin yaran Kano da aka kama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da hakan yake nufi shi ne ministocin za su iya sa ido a harkokin hukumomi da cibiyoyin da ke karkashin ma’aikatarsu.

Kafin yanzu, duk wasu muhimman takardu da suka fito daga manyan sakatorori su na zuwa ne teburin manyan ministoci.

Ikon kananan ministoci yanzu a gwamnati

Daga yanzu, karamin minista zai iya ba da umarni kuma ya amince da duk wani mataki na gwamnati a cibiyoyi da hukumomi.

Wata majiya ta ce shugaba Bola Tinubu bai jin dadin yadda aka maida kananan ministocin kasar tamkar ba su da amfani a doka.

A wannan tsari da ake tafiya, Sahara Reporters ta ce wasu ministocin sun zama ‘yan kallo, ba a cin moriyarsu da kyau a majalisa.

Wasu ‘yan majalisar zartarwa ta FEC sun zama ministocin gwamnati ne kurum a hoto.

Gwamnatin Tinubu ta zo da sabon tsari

Kara karanta wannan

"Za a zage ku," Abin da Tinubu ya faɗawa sababbin Ministoci bayan rantsar da su

Gwamnati ta ba kowane minista wuka da nama, ya taka rawa, abin da Dr. Joe Abbah ya yi maraba da shi da yake magana a X.

Mai taimakawa shugaban kasa wajen gudanar da tsare-tsaren gwamnati, Hadiza Bala Usman ta fara kawo wannan maganar.

Kananun ministocin su ne na aikin gona, tsaro, ilmi, harkokin Abuja, kiwon lafiya, fetur, fas, yaki da talauci da harkokin mata.

Akwai kananan ministocin kwadago, tattalin arziki, kasuwanci da kuma na raya gidaje.

Hadiza Bala Usman a mulkin Tinubu

Kun ji labari cewa a yanzu idan akwai wata kujerar da za a kira ‘ka fi minista’ a gwamnatin tarayya, Hadiza Bala Usman ce a kai.

Fitacciyar ‘yar siyasar kuma kwararriya a aikin gwamnati ta ke da ta-cewa a kan makomar ministocin Najeriya tun da aka nada ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng