Lakurawa Sun Yi Karfi a Sokoto, Suna Karbar Zakka, Sun Yiwa Al'umma Gargadi Mai Tsauri

Lakurawa Sun Yi Karfi a Sokoto, Suna Karbar Zakka, Sun Yiwa Al'umma Gargadi Mai Tsauri

  • Shugaban karamar hukumar Tangaza, Alhaji Isa Salihu Kalenjeni ya tabbatar da ayyukan yan kungiyar Lakurawa
  • Kalenjeni ya tabbatar da cewa matasan suna tilasta mutane biyan zakka da kwace dukiyoyin al'ummar yankunan
  • Hakan na zuwa ne bayan bullar kungiyar a kananan hukumomi biyar da ke jihar Sokoto a yan kwanakin nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Sabuwar kungiyar Lakurawas sun kara samun ƙarfi a kananan hukumomi biyar a Sokoto.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kungiyar Lakurawa ta fara zagayawa tana karbar Zakka daga hannun al'umma a yankunan.

Sabuwar kungiyar Lakurawa ta fara karbar Zakka a wasu yankunan Sokoto
Shugaban karamar hukuma a Sokoto ya tabbatar da ayyukan Lakurawa inda suke karbar Zakka. Hoto: Legit.
Asali: Original

Sokoto: Kananan hukumomi da Lakurawa suka mamaye

Vanguard ta ruwaito cewa yan kungiyar na yawo a kan babura kamar guda 10 zuwa 15 domin gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

Ire iren ta'addancin da sabuwar kungiyar Lakurawa ke yi a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kananan hukumomin da yan ta'addan suka mamaye sun hada da Tangaza da Illela da Gada da Binji da Silame.

Masu mazauna yankunan sun tabbatar da cewa matasan na magana da harsuna daban-daban domin isar da sakonsu.

Harsunan sun hada da Fulatanci da Turanci da Hausa da Kanuri da Tuba da Tuareg, cewar Sahara Reporters.

Yadda yan Lakurawa ke sheke ayarsu a Sokoto

Kungiyar tana yawo inda take karbar haraji da kuma kayan amfanin gona inda suke barazana ga wadanda ba su bayar ba.

Matasan sun gargadi mutane kan bin umarninsu domin tsira daga kwace musu dabbobinsu.

Shugaban karamar hukumar Tangaza, Alhaji Isa Salihu Kalenjeni ya tabbatar da zaman matasan a yankin.

"Suna tilasta mutane biyan zakka tare da fashi ga al'umma kan dukiyoyinsu."
"A kwanan nan sun yi wa wani fashin N2m a shagonsa da kwace motarsa sai da ya biya N350,000."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe bayin Allah ta hanya mai muni

- Alhaji Isa Salihu

Sokoto: Yadda Lakurawa ke sheke ayarsu

Kun ji cewa hukumomin Najeriya sun tabbatar da samuwar sabuwar kungiyar yan ta'addan Lakurawa a wasu sassa na Sokoto da Kebbi.

Mazauna wuraren da yan ta'addar ke zama sun bayyana yadda suka fara muzgunawa al'umma da ta'addancin da suke yi.

An kuma bayyana cewa yan ta'addar suna amfani da yare da dama wajen yin magana; Fulatanci, Kanuri, Turanci da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.