Mutanen Gari Sun Tunkari Mayakan Sabuwar Kungiyar Ƴan Ta'adda, An Rasa Rayuka
- Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Umar Tafida ya tabbatar da mutuwar mutum 15 a wani sabon harin ƴan ta'adda
- Rahoto ya nuna sabuwar kungiyar ƴan ta'adda, Lukurawa ne suka kai hari kauyen Mera a ƙaramar hukumar Augie
- Tuni dai aka yi jana'izar mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada kuma sarkin Argungu ya halarci wurin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Mayaƙan sabuwar ƙungiyar ta'addanci Lukurawa sun kai hari kauyen Mera da ke ƙaramar hukumar Augie a jihar Kebbi.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta'addan sun yi ajalin mutane 15 a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Yadda mutane suka tunkari mayaƙan Lukurawa
Wani babban mutum a garin, Alhaji Bashir Isah Mera (Yariman Mera), ya shaidawa Daily Trust cewa maharan sun shiga kauyen ana shirin tafiya sallar Juma'a
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ƴan ta'addan sun sace shanu 100 a harin, wanda hakan ya fusata mutane suka tunkari maharan aka yi musayar wuta.
Yariman Mera ya ce:
"Da jin haka sai ɗaruruwan mutanen garin suka taru suka bi su har daji da nufin kwato shanun. An yi musayar wuta tsakani wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 15 da Lukurawa biyu "
Gwamnatin Kebbi za ta ɗauki mataki
Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Umar Tafida ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Abubakar Tafida ya kai ziyara tare da yi wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin ta'aziyya da addu'ar Allah ya ba su hakuri da juriya.
Mataimakin gwamnan ya kuma tabbatarwa mazauna kauyen cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen gurfanar da waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.
Sarkin Argungu ya halarci jana'iza
A nasa ɓangaren, Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Mera, ya nuna alhininsa game da wannan mummunan harin, inda ya bukaci hadin kan jama’a da jajircewa.
Tuni dai aka yi jana'izar mutane 15 da aka kashe wanda mataimakin gwamna da kwamishinan 'yan sanda da kuma mai martaba sarki suka samu halarta.
Ƙungiyar ƴan ta'adda ta shigo Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojojin kasar nan ta tabbatar da shigowar sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda daga kasashen Mali da jamhuriyyar Nijar.
Sanarwar da daraktan yada labaran rundunar, Edward Buba ta fitar ta ce yan ta’addan sun yi sansani a Kebbi da Sakkwato.
Asali: Legit.ng