Afirka Ta Kudu da Wasu Kasashe 7 Sun Fara Shirin Sayen Futur daga Matatar Ɗangote

Afirka Ta Kudu da Wasu Kasashe 7 Sun Fara Shirin Sayen Futur daga Matatar Ɗangote

  • Matatar man Ɗangote ta fara tattaunawa da ƙasashe takwas waɗanda suka nuna sha'awar fara sayen mai daga wurinta
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da ƴan kasuwa da kamfanin mai na ƙasa NNPCL suka koma shigo da mai duk da matatar ta fara aiki
  • Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa ƙasashen da aka fara tattaunawar sun haɗa da Ghana, Angola, Namibiya da dai sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Matatar man Dangote na shirin fara jigilar man fetur zuwa kasashen ƙetare da suka haɗa da Afirka ta Kudu, Angola da Namibiya.

Masu kula da al'amuran matatar man attajirin ɗan kasuwar mai karfin ganga 650,000 suna ci gaba da tattaunawa da kasashen don fitar da mai.

Kara karanta wannan

"Shi ne mafi alheri" Sanata a Arewa ya fito da manufar cire tallafin mai a Najeriya

Matatar Man Ɗangote.
Kasashe 8 sun nuna sha'awar fara sayen man fetur daga matatar Ɗangote Hoto: Dangote Group
Asali: Getty Images

Wata majiya mai inganci da tushe a matatar Ɗangote ce ta tabbatar da haka ga daya daga cikin wakilan jaridar Punch a ranar Juma’a. 

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙasashe za su fara sayen mai daga matatar Ɗangote

Ta ce bayan waɗannan kasashe uku, akwai ƙarin wasu ƙasashe huɗu da suka fara tattaunawa da mahukuntan matatar Ɗangote don fara sayen man fetur.

Ƙasashen sun haɗa da Jamhuriyar Nijar, Chadi, Burkina Faso da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

An tattaro cewa akwai ƙarin kasashen da ake sa ran za su nuna sha'awar sayen mai daga matatar Ɗangote nan da ƴan watanni.

Kwanan nan ne aka ruwaito cewa kasar Ghana ta nuna sha'awar siyan man fetur daga matatar attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliku Ɗangote.

Ghana za ta daina shigo da mai daga turai

Shugaban hukumar man fetur ta Ghana, Mustapha Abdul-Hamid, ya ce ƙulla yarjejeniya da matatar man Dangote zai kawo karshen sayo man da suke yi daga Turai.

Kara karanta wannan

Wasu manyan jiga jigai da dubannin 'yan APC sun gaji da 'wahala', sun koma PDP

Ya ce ƙasar Ghana na shigo da man fetur na Dala miliyan 400 duk wata daga nahiyar Turai amma da zaran sun ƙulla kasuwanci da matatar Ɗangote za su daina zuwa Turai.

Majiya daga matatar Ɗangote ta ce:

"Ina fabbatar maku da cewa tattaunawa ta yi nisa da Ghana, Angola, Namibiya da Afirka ta Kudu, sannan kuma an ɓude tattaunawa da ƙasashen Nijar, Chadi, Burkina Faso da Afurka ta Tsakiya."

Matatar Ɗangote ta faɗi fatashin fetur

A wani labarin, kun ji cewa Matatar Dangote ta fito ta bayyana farashin da take siyar da man fetur ɗin da ta tace ga ƴan kasuwa.

Ɗangote ya bayyana cewa farashin da yake siyar da fetur ya fi arha fiye da wanda ake shigowa da shi daga ƙasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262