"Wata 3 Kenan Muna cikin Duhu" Gwamna Ya Koka kan Rashin Wutar Lantarki a Jiharsa
- Gwamna Douye Diri ya koka kan lalacewar wutar lantarki tsawon watanni uku a jihar Bayelsa saboda katsewar wasu na'u'rorin TCN
- Diri ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiki tare da kamfanin samar da wuta na ƙasa watau TCN domin gyara matsalar
- Ya ce jihar Bayelsa za ta fara samar da wuta ta ƙashin kanta ta yadda za ta daina dogaro da wutar da ake samarwa a ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana cewa watanni uku kenan babu wutar lantarki a jiharsa.
Gwamna Diri ya ce jama'ar Bayelsa sun rasa hasken wutar lantarki ne sakamakon lalata na'u'ron wuta na kamfanin rarraba wuta na ƙasa watau TCN.
Ya faɗi haka ne a wurin taron editocin Najeriya na 2024 wanda ya gudana a ɗakin taron tunawa da DSP Alamieyeseigha a Yenagoa ranar Juma'a, Leadership ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata 3 babu wutar lantarki a Bayelsa
Douye Diri ya ce tun da aka lalace waɗannan na'urori na TCN, jihar Bayelsa ta shiga duhun rashin wutar lantarki tsawon watanni uku kenan.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa a yanzu dai gwamnatinsa na aiki kafaɗa da kafaɗa da kamfanin TCN domin gyara wutar lantarki a Bayelsa.
Ya kara da cewa yana daga cikin ajendarsa mai taken, 'Assured', zai yi ƙoƙarin samar da wutar lantarki ta hanyar injinan gas domin jihar ta dogara da kanta.
Dalilin ɗauke wuta a jihar Bayelsa
A ruwayar Punch, Gwamna Diri ya ce:
"Ina so in sanar da ku cewa watakila kuna cikin otal din da akwai wuta, watanni uku kenan da Bayelsa ta shiga duhu, babu wutar lantarki.
"Akwai hasken wuta a otal, shiyasa ba za ku san cewa al’ummar jihar nan sun shafe watanni uku suna rayuwa ba tare da wutar lantarki ba."
"Dalili kuwa shi ne, wasu miyagu sun lalata na'urorin lantarki na kamfanin TCN, bayan wannan barna, jihar ta kasance cikin duhu har yau.
Gwamnoni sun fara kokarin samar da lantarkinsu
A wani labarin, kun ji cewa samun matsalar wuta a fadin Najeriya ta sanya jihohi fara neman mafita ga al'ummar su wajen kokarin samar da lantarki.
A wannan rahoton, mun tattaro muku yadda wasu gwamnoni suka fara ƙoƙarin samar da wutar lantarki ta kansu a jihohinsu.
Asali: Legit.ng