"Shi ne Mafi Alheri" Sanata a Arewa Ya Fito da Manufar Cire Tallafin Mai a Najeriya
- Sanata mai wakiltar Neja ta Gabas a majalisar dattawa, Sani Musa ya yi ƙarin haske kan cire tallafin mai da tsarin canjin Naira
- Sanata Sani Musa ya yi ikirarin cewa rabuwa da tallafin mai da ya jima yana laƙume kudi shi ne mafi alheri a Najeriya
- Ya bayyana cewa a yanzu jihohi na samun isassun kudi daga asusun tattara kuɗaɗen shiga na tarayya watau FAAC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin kudi, Sanata Sani Musa, ya yaba da tsare-tsaren tattalin arzikin shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Sani Musa ya yabawa tsare-tsaren da shugaban ƙasa ya ɓullo da su nusamman cire tallafin mai da kuma kyale Naira ta dogara da kanta a kasuwar canji.
Sanatan ya faɗi haka ne a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin a Channels tv ranar Juma'a, 8 ga watan Nuwamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda cire tallafi ya jefa mutane a wahala
Bayan ya shiga ofis a watan Mayun 2023, Shugaba Tinubu ya kawo karshen tallafin man fetur wanda ya daɗe dade yana laƙume biliyoyin daloli a shekara.
Jami’an gwamnatin Tinubu sun sha nanata cewa ana bukatar yin gyare-gyaren domin farfado da tattalin arzikin ƙasa mafi girman tattalin arziki a Afirka.
Amma dai tun wannan lokaci ƴan Najeriya ke fama da tsadar man fetur da hauhawar farashin kayan abinci.
"Cire tallafin mai shi ne mafi alheri'' - Sani
Da yake jawabi, Sanata Sani Musa mai wakiltar Neja ta Gabas ya bayyana cewa cire tallafin man fetur shi ne abu mafi alheri da ya faru da Najeriya.
Sanatan ya ce:
"Fatanmu shi ne duk abin da zamu yi kada ya ƙuntatawa ƴan Najeriya, abin da wannan gwamnatin ta yi na cire tallafin mai shi ne mafi alheri ga Najeriya.
Sani Musa ya soki gwamnatocin jihohi
Ɗan majalisar ya ƙara da cewa yanzu asusun tattara kuɗin shiga FAAC yana tara maƙudan kudi kuma yana tura wa jihohin isassun kudin da za a yi wa jama'a aiki.
Sani Musa ya caccaki gwamnatocin jihohi, inda ya ce da suna amfani da kuɗaɗen da suka samu yadda ya kamata, da komai ya tafi daidai, Daily Trust ta rahoto.
Matasa sun bukaci a kori shugaban NNPCL
A wani rahoton, an ji cewa Gungun masu zanga-zanga sun durfafi Majalisar Tarayya domin bukatar a kori shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari.
Matasan da ke wakiltar kungiyoyi sun bukaci Bola Tinubu ya gargadi Kyari kan tsare-tsare da za su jefa al'umma cikin kunci
Asali: Legit.ng