'Yan Sanda Sun Ragargaji 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane 21 da Aka Sace
- Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar daƙile harin ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Jibia da ke kan iyaka
- Jami'an tsaron sun yi nasarar fatatakar ƴan bindigan ne bayan sun kai hare-hare a wasu unguwanni Jibia a ranar Alhamis
- Ƴan sandan tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun kuma ceto wasu mutane 21 da ƴan bindigan suka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sanda a Katsina samu nasarar daƙile harin da ƴan bindiga suka kai a garin Jibia na jihar Katsina.
Rundunar ƴan sandan tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun kuma ceto mutane 21 da aka sace.
Kakakin rundunar ƴan sandan, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Katsina ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga
Jami'in ya bayyana cewa ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a unguwannin Ka'ida, Unguwar One Boy da Danmarke a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 9:15 na dare.
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa nan da nan tawagar jami'an tsaro ƙarƙashin DPO na Jibia, suka daƙile harin bayan an yi musayar wuta na fiye da awa ɗaya.
"Ƙarfin jami'an tsaron da ƙwarewarsu ta tilastawa ƴan bindiga arcewa ɗauke da raunuka masu yawa yayin da aka yi nasarar ceto mutane 16 da suka ɗauka."
"Abin takaici mamba ɗaya na rundunar KSWC da wani ɗan ɗaya sun rasa ransu a yayin artabun."
- ASP Abubakar Sadiq-Aliyu
Sadiq-Aliyu ya kuma ƙara da cewa wasu ƙarin mutum biyar da aka ceto sun samu raunuka inda aka garzaya da su zuwa asibiti domin ba su kulawar da ta dace.
Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun tafka danyen aiki bayan sun kai mummunan hari gidan wani mai fafutuka a jihar Katsina.
Yan bindigan sun kutsa gidan matashin dan fafutuka, Ibrahim Mai Kaita a gidansa da ke garin mai Turare a karamar hukumar, Dutsin-ma da ke Katsina, sannan suka kashe shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng