Gwamna Ya Duba Halin da Ake Ciki, Ya Yi Wa Masu Laifi Sama da 50 Afuwa

Gwamna Ya Duba Halin da Ake Ciki, Ya Yi Wa Masu Laifi Sama da 50 Afuwa

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi wa fursunoni 55 afuwa domin rage cunkoson gidajen gyaran hali a jihar Legas
  • Antoni janar kuma kwamishinan shari'a na Legas, Lawal Pedro ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Juma'a
  • Ya ce gwamnan ya ba da umarnin sakin fursunoni 40 nan take, sauran kuma sai sun kara wani wa'adi a gidan kaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya amince da sakin fursunoni 55 daga gidajen gyaran hali daban-daban a fadin jihar.

Gwamna Sanwo-Olu ya ɗauki wannan matakin ne bisa shawarwarin majalisar duba yiwuwar yi wa fursunoni afuwa ta jihar Legas.

Gwamna Babajide.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yafewa fursunoni 55 a jihar Legas Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Antoni-Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar, Lawal Pedro, SAN, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta shirya kama wani gwamnan PDP a Najeriya, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamma Sanwo-Olu ya saki fursunoni

Pedro ya ce Mai girma gwamna ya ba da umarnin sakin fursunoni 40 nan yake yayin da ragowar kuma za a sake su ne bayan aun karisa zaman watanni uku zuwa shida a gidan yari.

Lawal Pedro ya ce gwamnan ya yi wa masu laifin afuwa ne bisa tanadin sashe na 212 (1) & (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya 1999 da aka yi wa garambawul.

Dalilin yafewa fursunoni 55 a Legas

Ya kara da cewa hakan ya kuma yi daidai da alkawarin da gwamnan ya ɗauka na rage cinkoso a gidajen gyaran hali a Legas, rahoton Punch.

Haka nan kuma kwamishinan ya ce afuwar da aka yi wa fursunonin na cikin wani ɓangare na kokarin kawo sauye-sauye a sashen shari'a.

Lawal ya ce an duba abubuwa da dama wajen zaƙulo waɗanda suka cancanci a yi wa afuwa, daga ciki an duba halaye, ɗabi'u, shekaru, lafiya da daɗewa a gidan yari.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sanda za ta tura jami'ai 22000 zuwa Kudancin Najeriya, an gano dalili

"Za a saki fursunonin ne da zaran an kammala bin tsare-tsaren gudanarwa na gidan gyaran hali," in ji shi.

Gwamnatin Legas ta rufe wuraren ibada

A wani rahoton an ji cewa Gwamnatin Legas ta ce a shekarar da ta gabata kaɗai ta rufe Masallatai, Majami'u da wasu wurare saboda yawan hayaniya.

Shugaban hukumar kare muhalli, Dr. Babatunde Ajayi ya ce tun farko sun gargaɗi shugabannin addinai kan cika ƙarar lasifika.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262