Zanga Zanga: 'Yan Majalisa Sun Mika Bukata wajen Gwamnati kan Yaran da Aka Tsare
- Ƙungiyar marasa rinjaye na majalisar wakilai ta yabawa Bola Tinubu kan ba da umarnin sakin yaran da aka tsare kan zanga-zanga
- Ƴan majalisar tarayyar sun buƙaci a hukunta duk masu hannu a tsare yaran ba bisa ƙa'ida ba na tsawon kwanaki
- Sun kuma buƙaci a biya diyya ga yaran domin rage musu raɗaɗin wahalar da suka sha a lokacin da suke a tsare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar marasa rinjaye na majalisar wakilai ta yi magana kan sakin yaran da aka tsare saboda shiga zanga-zanga.
Ƴan majalisar sun buƙaci a biya diyya ga ƙananan yaran waɗanda aka tsare bisa zargin shiga zanga-zangar #EndBadGovernance.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda da mataimakinsa, Aliyu Sani Madakin Gini, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ƴan majalisa suka ce kan tsare yara?
Ƴan majalisar sun buƙaci a gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru dangane da cafkewa da zargin azabtar da ƙananan yaran masu zanga-zangar, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
Ƙungiyar ta kuma yabawa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa bayar da umarnin a gaggauta sakin yaran waɗanda rundunar ƴan sandan Najeriya ta tuhume su da laifukan ta’addanci da cin amanar ƙasa.
"Dole a hukunta duk wani mutum ko wata hukuma da ke da alhakin tsare waɗannan yaran na kusan kwanaki 95 a lokacin da ya kamata a ce su na makaranta ko wajen koyon sana'o'i, domin zama kashedi ga saura."
"Duba da irin wahala da ƙalubalen rashin lafiya da yaran suka fuskanta, muna kira da a ba su cikakkiyar kulawa ta fannin lafiyarsu yayin da aka mayar da su wajen iyalansu."
"Muna kuma kiran da a gaggauta ba yaran da iyalansu diyya domin rage musu wahala, raɗadi da ƙuncin da suka shiga a lokacin da ake tsare da su ba bisa ƙa'ida ba."
- Hon. Kingsley Chinda
Gwamna ya tarbi yaran da aka tsare
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta karbi bakuncin yara 39 da aka sako daga Abuja kan zargin zanga-zanga.
Mai girma Gwamna Uba Sani shi ya karbi yaran inda aka yi nasarar hada su da iyayensu bayan shigowa jihar Kaduna a makon nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng