Bayan Ɓullar Lakurawa, an Yaye Askarawan Yaƙi 500 a Katsina

Bayan Ɓullar Lakurawa, an Yaye Askarawan Yaƙi 500 a Katsina

  • Gwamna Dikko Umaru radda ya halarci bikin yaye askarawan jihar Katsina karo na biyu da ya gudana a sansanin hukumar NSCDC
  • An yaye askarawa kimanin 500 da za su rika taimakawa jami'an tsaro wajen yaki da yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Katsina
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamna Dikko Radda ya tanadi motoci, babura da sauran kayan aiki da askarawan za su rika aiki da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - A yau Juma'a, 8 ga watan Nuwamba gwamnati ta yaye askarawan jihar Katsina karo na biyu.

An ruwaito cewa gwamna Dikko Umaru Radda ya halarci bikin yaye askarawan da ya gudana a sansanin hukumar NSCDC na jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bude tashoshin mota domin rage raɗaɗi tsadar fetur

Askarawa
An yaye askarawa 500 a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta samo bayanai kan yadda bikin ya gudana ne a cikin wani sako da hadimin gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yaye askarawa 500 a Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta kammala ba askarawa kimanin 500 horo domin saka hannu wajen yakar yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Shirin samar da askarawa na cikin kokarin gwamna Radda na ba mutanen gari damar shiga yaki da ake da yan bindiga a jihar Katsina.

Wannan shi ne karo na biyu da gwamnatin Katsina ke samar da askarawa da za su saka hannu ga jami'an tsaro wajen yaki da yan ta'adda.

An tanadi kayan aiki ga askarawa

Biyo bayan kammala ba askarawan horo, gwamna Dikko Umaru Radda ya tanada musu wadatattun kayan aiki.

Gwamnatin Katsina ta tanadi motoci, babura da dama da za su taimakawa askarawan wajen yaki da miyagu.

Kara karanta wannan

An yi artabu da Askawaran Zamfara, 'yan ta'adda sun ji babu dadi

Al'umma na sa ran cewa askarawan za su yi matukar taimakawa wajen yaki da yan bindiga musamman yanzu da aka samu bullar Lakurawa a Arewa ta Yamma.

Yan bindiga sun kai hari Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa wasu miyagu yan bindiga sun kai hari garin Mai Turare da ke karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina.

An ruwaito cewa mutanen dauke da miyagun makamai sun farmaki gidan wani sanannen dan fafutuka mai suna Ibrahim Mai Kaita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng