Gwamna a Arewa Ya Ba da Umarnin Gyara Asibitoci 34, Ya Ƙara Ɗaukar Alƙawari Kafin 2027
- Gwamna Dikko Radda ya kara ba da umarnin sabunta ƙananun asibitoci 34 tare ɗaga darajarsu a faɗin jihar Katsina
- Wannan na zuwa ne a lokacin da aikin gyaran asibitocin gwamnati sama da 100 ya yi nisa a faɗin ƙananan hukumomi 34
- Dikko Radda ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kowace gunduma na da akalla asibiti ɗaya mai ingantattun kayan aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Gwamna Malam Dikko Raɗɗa ya waiwaiyi ɓangare kiwon lafiya, ya amince da gyaran ƙananun asibitoci PHC guda 34 da ɗaga darajarsu a Katsina.
Wannan dai kari ne bayan waɗanda ake kan aikin gyaransu 102 tare da inganta ayyukansu na kiwon lafiya a faɗin ƙananan hukumomi 34.
Kamar yadda Channels tv ta kawo, Dikko Raɗɗa ya ce wannan na ɗaya daga cikin burinsa na inganta harkokin kiwon lafiya a zangon mulkinsa na farko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Dikko ya kara ɗaukar alƙawari
Ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kowace gunduma daga cikin gundumomi 361 da ake da su a Katsina tana da asibitin da yake aiki sosai kafin zangon mulkin farko ya ƙare.
Gwamna Radda ya yi wannan jawabi ne ranar Alhamis da yake duba ayyukan gyaran dakunan shan magani da ke gudana a fadin kananan hukumomi bakwai na shiyyar Daura.
Gwamna Radda ya tattauna da majinyata a Daura
Yayin wannan ziyara dai, gwamnan ya tattauna da marasa lafiya da malaman asibiti domin jin matsalolin da ake fuskanta da hanyar da ya kamata a gyara.
A cewarsa, bayan wannan tattaunawa ya gano abubuwa da dama kuma ya ɗauki matakan da yake ganin za su inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar Katsina.
Wane irin gyara ake yi wa asibitoci a Katsina?
A wata hira da shugaban hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta Katsina, Dr Shamsuddin Yahaya, ya bayyana sha'anin lafiya a matsayin ginshikin da ya kamata a tabbatar da zauna daidai.
Ya tunatar da cewa a makonni biyun da suka gabata Gwamna Radda ya zagaya asibitoci 11 a shiyyar Funtua.
Dr. Shamsuddin ya ce gyaran da ake yi wa asibitocin ya ƙunshi gina gidajen zaman ma'aikata, kayan aiki da wuraren duba marasa lafiya.
Gwamnatin Katsina ta buɗe tashoshin mota
A wani labarin, an ji cewa gwamnatin Katsina karkashin Dikko Umaru radda ta bude tashoshin mota guda biyu domin rage radadin tsadar rayuwa ga talakawa.
Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da sayen motoci domin rage radadin cire tallafin mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng