Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa, Sun Bindige Dan Sanda, Sun Sace Yan Kasashen Waje

Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa, Sun Bindige Dan Sanda, Sun Sace Yan Kasashen Waje

  • Wani sifetan dan sanda ya rasa ransa yayin da yan bindiga suka kai wani karamin hari a Rivers a Kudancin Najeriya
  • Maharan sun kai hari ne a sansanin Quarry da ke karamar hukumar Akamkpa a ranar Alhamis 7 ga watan Nuwambar 2024
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce bayan kisan dan sanda an sace wasu mutanen kasar China

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Yan bindiga sun kai kazamin hari a ƙaramar hukumar Akamkpa da ke jihar Rivers inda suka hallaka wani dan sanda.

Yayin harin, maharan sun yi ajalin sufetan san sanda tare da awon gaba da wasu yan kasar China guda biyu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe bayin Allah ta hanya mai muni

Yan bindiga sun hallaka sufetan dan sanda a Rivers
Yan bindiga sun yi ajalin sufetan dan sanda da sace wasu yan kasar China a Rivers. Hoto: @PoliceNG.
Asali: Twitter

Yan bindiga sun sace yan China 2

Premium Times ta ruwaito cewa maharan sun kai harin ne a yammacin jiya Alhamis 7 ga watan Nuwambar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar yan sanda, SP Nelson Okpabi ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a yau Juma'a a birnin Calabar.

Okpabi ya ce an sace yan kasar China biyu tare da wani dan Najeriya guda daya bayan kisan dan sandan, cewar Daily Post.

Sanarwar ta ce maharan sanye da kayan sojoji sun tafi da bindiga kirar AK-47 na dan sandan da suka hallaka.

Yan sanda sun sha alwashi kan yan bindiga

Rundunar ta ce yan bindiga sun samu shiga sansanin Quarry bayan sakacin wani ma'aikacin wurin.

Sai dai mataimakin sifetan yan sanda a yankin, Jonathan Towuru ya umarci kaddamar da bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun gwabza faɗa da yan bindiga, an kashe wasu miyagu

Towuru ya sha alwashin zakulo yan bindigan tare da tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci daidai da laifinsu.

Ambaliya ya tarwatsa mutane a Rivers

Kun ji cewa mutane masu yawa sun rasa matsugunansu bayan an samun ambaliyar ruwa a ƙaramar hukumar Obio/Akpor ta jihar Rivers.

Jama'a sun koka da cewa ambaliyar ruwan ta tilasta musu barin gidajensu bayan macizai sun mamaye inda suke rayuwa ta ko ina a yankin.

Mutanen da ke yankin Rumaholu-Nkpolu sun yi kira ga gwamnatin jihar kan ta gina musu magudanun ruwa domin kare faruwar hakan a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.