Likitoci Sun Gana da Gwamnan Kano, Sun Canza Matsaya kan Shiga Yajin Aiki
- Kungiyar likitocin Najeriya ta dakatar da yajin aikinta, ta dawo da ayyuka a asibitin kwararru na Murtala Muhammad, Kano
- Gwamnan Kano ya gana da shugabannin kungiyar, inda aka warware matsalar da ke tsakanin wata likita da kwamishiniyar jihar
- Shugaban kungiyar, Dakta Abdulrahman Ali ya gode wa gwamnan bisa saurin daukar mataki, inda ya aika sako ga al'umar jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta dakatar da yajin aikinta tare da dawo da cikakken aiki a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
Wannan ci gaban ya biyo bayan shiga tsakani da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, bayan ganawarsa da shugabannin kungiyar a ranar Alhamis.
An daidaita tsakanin likita da kwamishiniya
Shugaban kungiyar, Dakta Abdulrahman Ali, ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust wannan ci gaban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakta Abdulrahman ya bayyana cewa an samu daidaito a matsalar da ta taso tsakanin wata likita a asibitin Murtala da wata kwamishiniya.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa mai zurfi da gwamnan.
Likitoci sun jinjinawa gwamnan Kano
Dakta Abdulrahman ya yaba wa gwamnan bisa saurin daukar matakin da ya yi, wanda ya hana ci gaba da samun rikici a fannin kiwon lafiyar jihar.
Ya kuma shawarci al'ummar Kano su mika koke-kokensu ta hanyoyin da suka dace, inji rahoton Vanguard.
Shugaban kungiyar ya tabbatar da cewa za a duba kuma a magance duk wani rikici tsakanin marasa lafiya da ma'aikatan kiwon lafiya cikin adalci.
Yadda likitocin Kano suka tsunduma yajin aiki
Tun da fari, mun ruwaito cewa kungiyar likitocin Najeriya (NMA) sun sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani a asibitin Murtala Muhammad da ke Kano.
Likitocin sun bayyana cewa shiga yajin aikin ya zama dole sakamakon cin zarafin wata abokiyar aikinsu da kwamishiniyar jin kai ta jihar ta yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng