"Kun Yi Bajinta": Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Halin 'Yan Najeriya da ya Cancanci Yabo
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yaba da juriyar ƴan Najeriya kan halin matsin tattalin arziƙin da aka shiga a ƙasar nan
- Ministan kuɗi, Wale Edun ya bayyana cewa sauye-sauyen da aka yi wa tattalin arziƙin ƙasar nan sun kusa haifar da ɗa mai ido
- Edun ya yi nuni da cewa lokacin shan wuya ya zo ƙarshe yanzu abin da ya rage shi ne fara ganin amfanin sauye-sauyen da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi magana kan tsadar rayuwar da ƴan Najeriya ke fuskanta sakamakon manufofin Shugaba Bola Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta ce ta yaba da juriyar da ƴan Najeriya suka yi kan manufofi da sauye-sauye kan tattalin arziƙi, wanda a cewarta, sun fara haifar da ɗa mai ido.
Ministan kuɗi da harkokin tattalin arziƙi, Wale Edun ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kuɗi, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya ta yabawa ƴan Najeriya
A cewar ministan, matsalolin da ƴan Najeriya suka fuskanta sakamakon sauye-sauyen da aka ɓullo da su, sun zo ƙarshe.
Wale Edun ya ce alamu sun nuna cewa daɗi na nan tafe, rahoton Tribune ya tabbatar.
"Sauye-sauyen guda biyu masu muhimmanci da suka shafi gyara kasuwar man fetur da kuɗin ƙasashen waje, yanzu suna a matakin da za a fara ganin sakamako mai kyau."
"Waɗannan ginshiƙai guda biyu na sauye-sauyen tattalin arziƙin da suka samu kyakkyawan tsari a yanzu suna nuna gwamnati za ta samu ƙarin kuɗaɗen shiga."
"Farfaɗo da kuɗin NNPC da haɓaka tattalin arziƙi, ta fuskar jawo masu zuba hannun jari da samar da ayyukan yi."
"Ina ganin muna buƙatar mu yabawa ƴan Najeriya kan yadda suka yi haƙuri har zuwa wannan matakin da za a fara ganin fa'idar hakan."
- Wale Edun
Gwamnatin tarayya ta magantu kan tallafin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan kudi da harkokin tattalin Arziki, Wale Edun, ya ce babu gudu babu ja da baya game da manufofin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Mista Wale Edun ya tabbatar da cewa shugaban ƙasa ba zai janye kudirinsa na cire tallafin man fetur da canza tsarin canjin kuɗi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng