Wasu Jihohin Arewa da Kudu da Suka Fara Kokarin Samar da Wutar Lantarkinsu

Wasu Jihohin Arewa da Kudu da Suka Fara Kokarin Samar da Wutar Lantarkinsu

  • Samun matsalar wuta a fadin Najeriya ta sanya jihohi fara neman mafita ga al'ummar su wajen kokarin samar da lantarki
  • Dama dai gwamnatin tarayya ta yi kira ta bakin ministan makamashi, Adebayo Adelabu kan muhimmancin samar da wuta a jihohi
  • A wannan rahoton, mun tattaro muku yadda wasu gwamnoni suka fara ƙoƙarin samar da wutar lantarki ta kansu a jihohinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - A wata ziyara da ya kai jihar Kano, ministan makamashin Najeriya, Adebayo Adelabu ya yi kira ga gwamnoni kan samar da wuta a jihohi.

Biyo bayan hakan, wasu gwamnonin jihohi sun fara ƙoƙarin samar da wuta a jihohinsu domin rage dogaro da wutar gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Gwamna zai dakile matsalar lantarki, an hada kai da kamfanin China

Gombe
Za a samar da lantarki a Gombe da Ekiti. Hoto: Isma'ila Uba Misilli|Biodun Oyebanji
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku rahoto a kan ƙoƙarin da gwamnonin Gombe da Ekiti ke yi wajen samar da wuta a jihohinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙoƙarin samar da wuta a jihar Gombe

Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya fara kokarin samar da wuta mai amfani da hasken rana a jihar.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce zai yi amfani da dokar gwamnatin tarayya da ta ba jihohi damar samar da lantarki domin kansu.

Gombe ta yi yarjejeniya da kamfanin Sin

A kokarin samar da wutar lantarki a jihar, kwamishinan makamashi na jihar Gombe, Sanusi Ahmad Pindiga ya rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanin kasar Sin.

Gombe
Gwamnatin Gombe ta yi yarjejeniya da kamfanin 18th Engineering. Hoto: Isma'ila Uba Misilli
Asali: Facebook

Daraktan yada labaran gwamnatin Gombe, ya wallafa a Facebook cewa Sanusi Ahmad Pindiga ya rattaba hannu kan yarjejeniyar wutar ne da kamfanin 18th Engineering.

Karfin wutar da za a samar a Gombe

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe uba da yaƴansa 2

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya tabbatar da cewa a karkashin yarjejeniyar za a samar da wutar sola mega watt 100 a Gombe.

Inuwa Yahaya ya bayyana cewa bayan samun fahimtar juna da kamfanin 18th Engineering, saura a saki kudi ne da kuma fara aiki.

Alfanun da wutar Gombe za ta haifar

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa wutar za ta rage matsalolin lantarki a jihar da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.

"Idan aka ƙaddamar da wannan aikin, muna sa ran zai samar da ayyukan yi, jawo masu zuba jari da samar da ingantaccen makamashi da zai bunkasa Gombe da Arewa maso Gabas.
Shirin ya nuna kokarinmu na samar da makamashin ta ingantacciyar hanyar da ta dace da muhalli."

- Inuwa Yahaya

Manajan kamfanin 18th Engineering, Xue Dewen ya tabbatar da cewa ya shirya tsaf domin samar da wutar sola mai inganci a jihar Gombe.

Kokarin samar da wutar lantarki a Ekiti

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta kawo hanyar da Arewa za ta rage samun rashin wuta

Gwamantin jihar Ekiti ta fara wani yunkurin samar da wutar lantarki duk da cewa ba da kanta za ta yi aikin ba.

A Ekiti, an ba kamfanoni 14 damar samar da wutar lantarki da rarraba ta ga al'ummar jihar.

Rahoton Premium Times ya nuna cewa kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Ekiti, Mobolaji Aluko ne ya sanar da hakan.

Yadda za a samar da wuta a Ekiti

Gwamnatin Ekiti ta ba kamfanoni izinin samar da wuta ne da kuma rarraba ta ga mutane domin cin riba.

A karkashin haka, kamfanonin za su kafa ƙananan tashoshin rarraba wuta da samar da mitar wutar lantarki ga al'umma.

Adadin wutar da za a samar da Ekiti

Kamfanoni 14 da gwamnati ta ba izinin samar da wuta a Ekiti za su samar da lantarki mega watt 120.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a yanzu haka tana samun wuta mega watt 20 zuwa 25 daga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

'Kaduna kun ba mu kunya': An yi ce ce ku ce kan bidiyon murnar dawo da wutar lantarki

Bambancin aikin wutar Gombe da Ekiti

Gwamnatin jihar Gombe da kanta za ta samar da wutar lantarki, a daya bangaren kuma yan kasuwa ne za su samar da wutar.

Haka zalika za a samar da lantarki mega watt 100 ne a jihar Gombe alhali mega wat 120 za a samar a jihar Ekiti.

Legit ta tattauna da Abdulmutallib Yahaya

Wani mai aikin walda, Abdulmutallib Yahaya ya zantawa Legit cewa idan har gwamnan Gombe ya samar da wuta to su kam ya share musu hawaye.

Abdulmutallib Yahaya ya ce za su yi farin ciki da wutar domin a yanzu haka ayyukansu da dama sun tsaya saboda matsalar lantarki.

Kwamitin lantarki ya fitar da rahoto

A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin gano dalilin yawaitar matsalar wutar lantarki a kasar nan ya fitar da rahotonsa.

Injiniya Nafisatu Asabe Ali ce ta ke jagorantar kwamitin da ake ganin zai fadi matsalolin da bangaren lantarki ke fuskanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng