'Ban Tsoron EFCC': Gwamnan PDP Ya Bugi Kirji, Ya Fadi Abin da Zai Yi Idan Suka Neme Shi

'Ban Tsoron EFCC': Gwamnan PDP Ya Bugi Kirji, Ya Fadi Abin da Zai Yi Idan Suka Neme Shi

  • Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana irin ayyukan alheri da ya yi a mulkinsa musamman a bangaren ilimi
  • Obaseki ya ce yayin mulkinsa a jihar Edo ya mayar da hankali wurin ayyukan alheri ba tare da sauraran masu surutu ba
  • Gwamnan ya ce bai tsoron EFCC ko kadan saboda babu abin da yake boyewa kuma da kansa zai mika wuya idan aka buƙata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki ya ce kwata-kwata bai tsoron hukumar yaki da cin hanci ta EFCC.

Gwamnan ya ce da kansa zai mika wuya idan har hukumar ta gayyace shi bayan kammala mulkinsa.

Gwamnan PDP ya yi magana kan tuhumar EFCC
Gwamna Godwin Obaseki ya ce bai tsoron EFCC su kama shi bayan kammala mulki. Hoto: Governor Godwin Obaseki.
Asali: Facebook

Gwamna Obaseki ya ce ya shuka abin kirki

Kara karanta wannan

"Ban sani ba sai daga baya," Gwamna Abba ya faɗi abin da ya faru da yaran Kano

Obaseki ya bayyana haka a wani babban taro a Abuja a jiya Laraba 6 ga watan Nuwambar 2024, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Obaseki ya ce ba shi da wani kulli da ya aikata a mulkinsa tsawon shekaru takwas da zai saka shi tsoron EFCC.

Ya bayyana irin ayyukan alheri da gwamnatinsa ta aiwatar musamman a bangaren ilimi, Daily Post ta ruwaito wannan.

Gwamnan Edo ya soki tsarin jam'iyyar APC

Har ila yau, ya caccaki jam'iyyar APC kan shiga abin da bai shafe ta ba madadin shawo kan matsalar da yan kasa ke ciki.

"Ba na tsoron hukumar EFCC ko kadan, a kan menene zan ji tsoronta, lokacin da na zo mulki na mayar da hankali sosai ban tsaya sauraran korafe-korafe ba."
"Idan hukumar EFCC ta gayyace ni, da kai na zan je saboda na yi abin kirki babu abin da zan boye."

Kara karanta wannan

"Na gamsu da ayyukan da na yi," Gwamna ya ce ya cika alkawurran da ya ɗauka a kamfe

- Godwin Obaseki

Edo: Gwamna ya cika baki da ayyukansa

Kun ji cewa Gwamnan Edo mai barin gado, Godwin Obaseki na ci gaba da buɗe ayyukan da ya kammala yayin da yake shirin miƙa mulki.

Obaseki ya bayyana cewa ya gamsu da ayyukan da ya yi wa al'umma a mulkinsa, inda ya ce ya cika alƙawurran da ya ɗauka.

Nan da wasu ƴan kwanaki Obaseki zai sauka daga kan madafun iko, ya miƙa mulki ga zababben gwamnan Edo, Monday Okpebholo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.