DHQ Ta Bayyana Sunayen Mutum 9 da Take Nema Ruwa a Jallo kan Ta'addanci a Arewa
- Hedkwatar tsaro DHQ ta ayyana neman wasu mutuane ruwa a jallo kan zargin ta'addanci da tsattsauran ra'ayi a Arewa maso Gabas
- Mai magana da yawun hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba ya sanar da haka a taron manema labarai a hedkwatar tsaro da ke Abuja
- Buba ya ce dukkan wanɗanda ake zargin sun fito ne daga Arewa maso Gabashin Najeriya, ya jero sunayensu domin ganin an kama su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana mutum tara a matsayin waɗanda take nema ruwa a jallo kan zarge-zargen ta'addanci da tada kayar baya.
Mai magana da yawun hedikwatar Manjo Janar Edward Buba ne ya jero sunayen ƴan ta'addan guda tara da ake nema ruwa a jallo a Abuja ranar Alhamis.
DHQ ta jero sunayen ƴan ta'addan da take nema
The Nation ta tattaro cewa waɗanda ake zargin sun haɗa da Abu Khadijah, Abur Rahman, Dadi Gumba, Abu Yusuf da Musa Wa’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran waɗanda ake zargi da hannu a ta'addanci da tsattsauran ra'ayin addini sune, Usman Kanin Shehu, Ibrahim Suyeka, Ba Sulhu da kuma Idris Taklakse.
Edward Buba ne ya sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai a hedikwatar tsaro da ke birnin tarayya Abuja.
Kakakin DHQ ya ce dukkan ƴan ta'addan da ake neman sun fito ne daga shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.
Karanta wasu labaran rundunar sojojin Najeriya a nan:
- Dakarun sojoji sun samu babbar nasara, sun kashe ƴan bindiga sama da 400
- COAS: Muƙaddashin hafsan sojojin ƙasa da Tinubu ya naɗa ya kama aiki a Abuja
- Sojoji sun samu gagarumar nasara, an kashe hatsabiban 'yan bindiga a Arewa
DHQ ta ce wasu ƴan ta'adda na son miƙa wuya
A wani labarin, an ji cewa rahotanni sun tabbatar da wasu yan bindiga da dama sun nuna sha'awar ajiye makamansu musamman a Arewacin Najeriya.
Rundunar tsaro ta tabbatar da hakan inda ta ce shugabannin yan ta'addan a Arewa ta Tsakiya sun nuna sha'awar hakura da ta'adi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng