Kwana Ya Kare: Jami'in Dan Sanda Ya Rasu a Wani Hatsarin Mota
- Wani jami'in ɗan sanda ya ransa a wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya
- Ɗan sandan ya rasa ransa ne bayan wasu motocin da suka yi hatsari sun haɗe da shi lokacin da yake tafiya a kan babur ɗinsa
- Babban sakataren hukumar ba da agajin gaggawa a Legas (LASEMA), ya tabbatar da aukuwar hatsarin da ya jawo rashin rai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Wani jami'in ɗan sanda ya rasa ransa a wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a jihar Legas.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (LASEMA) ta ce hatsarin ya ritsa da ɗan sandan ne a kan Gadar Kara a yankin Berger na jihar.
Babban sakataren hukumar LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hatsarin mota ya yi silar rasuwar ɗan sanda
Sakataren ya bayyana cewa hatsarin ya ritsa da wata motar tirela ɗauke da kaya da motocin bas ƙirar Toyota Hiace da Mercedes.
Olufemi Oke-Osanyintolu ya bayyana cewa binciken hukumar ya nuna cewa motar tirelar ta faɗa kan motar bas ta Mercedes lokacin da suke tafiya.
Ya ce daga nan sai ta ƙwace daga kan hanyar ta murƙushe motar bas ta Toyota Hiace da aka ajiye a gefen titi.
Ya bayyana cewa jami'in ɗan sandan wanda yake aiki da Mopol 20, motocin sun haɗe da shi ne yayin hatsarin lokacin da yake tafiya a kan babur ɗinsa.
Olufemi Oke-Osanyintolu ya bayyana cewa an kai gawar ɗan sandan zuwa ofishin ƴan sanda na Ojodu.
Tankar mota ta fashe
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar tanka maƙare da man fetur ta fashe ta kama da wuta a Maitama, ɗaya daga cikin manyan unguwanni a babban birnin tarayya Abuja.
Bayanai sun nuna wasu mutane da ke cikin motar haya a kusa da tankar sun samu raunuka daban-daban sakamakon fashewar yau Litinin, 23 ga watan Satumba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng