Gwamnati Ta Dauko Aiki, Mata Za Su Fara Haihuwa Kyauta a Asibiti a Najeriya
- Ministan lafiya da walwalar jama'a, Farfesa Muhammad Ali Pate ya bayyana shirin gwamnati a kan matan Najeriya
- A wani taro na hadin gwiwa da ake yi duk shekara, Farfesa Muhammad Ali Pate ya ce shirin zai rage mutuwar mata
- Ya ce alkaluma sun nuna yadda ake asarar rayukan mata da jariransu yayin haihuwa, shi ya sa aka dauki matakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana sabon shirin da zai inganta lafiyar mata masu haihuwa a fadin Najeriya.
Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate ne ya bayyana gagarumin tsarin da zai shafi dukkanin matan Najeriya da ke bukatar cin gajiyar shirin.
A sakon da ofishin yada labaran shugaban kasa, Bola Tinubu ya wallafa a shafin X, an bijiro da tsarin ne domin rage yawaitar mutuwar mata yayin haihuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin gwamnatin Tinubu kan matan Najeriya
Gwamnatin tarayya ta ce za a rika yi wa dukkanin mata masu juna biyu da ke bukatar tiyata domin haihuwa aiki kyauta a kasar nan.
Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate ya ce wannan na daga shirin gwamnati na rage yawan mutuwar mata masu juna biyu na MAMII.
Gwamnatin Tinubu ta damu da mutuwar mata
Gwamnatin tarayya ta ce kasar nan na fuskantar gagarumin kalubalen mutuwar mata a lokutan haihuwa, kamar yadda wani Shehu Hassan Makwallah ya wallafa a Facebook.
A cewar gwamnati, mata 512 a cikin 100,000 ke rasa ransu yayin haihuwa, inda ake rasa jarirai 41 a cikin guda 1,000 da aka haifa.
Ministan harkokin lafiya da walwalar jama'a na ganin shirin zai rage adadin wadanda ke mutuwa a lokacin haihuwa, amma ba a fitar da karin bayani kan shirin na.
Gwamnati za ta kara albashin ma'aikatan asibiti
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta dauki alkawarin kara albashin ma'aikatan lafiya domin kashe kwadayinsu na tafiya kasashen waje neman aiki da albashi mai kyau.
Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate ne ya shaida haka, tare da cewa gwamnati na daukar matakan inganta bangaren lafiya a kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng