Sun Sha Wuta: Manyan Yan Bindiga Sun Fara Neman Mika Wuya a Ajiye Makamai

Sun Sha Wuta: Manyan Yan Bindiga Sun Fara Neman Mika Wuya a Ajiye Makamai

  • Rahotanni sun tabbatar da wasu yan bindiga da dama sun nuna sha'awar ajiye makamansu musamman a Arewacin Najeriya
  • Rundunar tsaro ta tabbatar da hakan inda ta ce shugabannin yan ta'addan a Arewa ta Tsakiya sun nuna sha'awar hakura da ta'adi
  • Daraktan yada labaran rundunar, ya ce shugabannin da jagororin yan bindiga sun zabi ajiye makami saboda wuta da suke karba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar tsaro a Najeriya ta yi magana kan neman sulhu da wasu yan bindiga ke yi a Arewacin kasar.

Rundunar ta ce shugabannin yan ta'adda da dama a Arewa ta Tsakiya suna neman samun dama domin ajiye makamansu.

Kara karanta wannan

"Ban sani ba sai daga baya," Gwamna Abba ya faɗi abin da ya faru da yaran Kano

Yan bindiga sun fara neman ajiye makamansu
Rundunar tsaro ta tabbatar da cewa wasu yan ta'adda na neman mika wuya ga sojoji. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Ta'addanci: Rundunar sojoji sun bude kofar sulhu

Premium Times ta ruwaito cewa daraktan yada labaran rundunar, Edward Buba shi ya tabbatar da haka a birnin Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edward Buba ya ce rundunar ta bude kofa ga duk yan bindiga ko shugabanninsu da ke da sha'awar ajiye makamansu.

Har ila yau, Buba ya ce yan ta'addan sun sani ba za su iya karawa da sojoji ba shiyasa suke neman mafita, Daily Post ta ruwaito hakan.

Yadda yan bindiga ke neman miƙa wuya

"Zabin da aka ba su shi ne su mika wuya ko kuma su hallaka a filin daga saboda barin wuta daga rundunar sojoji."
"A dalilin haka, wasu kwamandojinsu da shugabanni da kuma yan ta'addan sun zabi su ajiye makamansu domin zaman lafiya."
"Mu na kokarin bude kofa ga yan bindiga da ke nuna sha'awar ajiye makamansu saboda zaman lafiya."

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun fadi dalilin Tinubu na sakin kananan yaran da aka kama

- Edward Buba

Yan Najeriya sun yi alhinin rasuwar Lagbaja

Kun ji cewa ana cigaba da alhini da tura sakon jaje ga Bola Bola Tinubu da sauran yan Najeriya kan rasuwar hafsan sojoji, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja.

Mazauna yankin Birnin Gwari da iyakar jihar Niger inda ake fana da rashin tsaro sun nuna damuwa kan babban rashin da aka yi a Najeriya.

Kungiyar BG-NI CUPD ta ce yan Najeriya za su yi kewar Lagbaja musamman wadanda ke fama da rashin tsaro a yankunansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.