Lagbaja: Za Ayi Zazzagar da Za Ta Taba Janarori, Tinubu Zai Nada Hafsun Soja
- Bayan rasuwar babban hafsan sojojin kasar nan, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ana jiran a fadi wanda zai maye gurbinsa
- Ana sa ran za a bayyana Laftanar Janar Oluyede a matsayin sabon babban hafsan soji bayan jim kadan daga likkafarsa a rundunar
- Rahotanni na nuni da cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai ayyana Janar Oluyede ba har sai majalisar ta amince da nadin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ana sa ran sake fasalta rundunar sojojin kasar nan, yayin da za a sauya wa wasu daga cikin manyan janaral a rundunar wurin aiki.
Wannan na zuwa bayan an sanar da rasuwar babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja a ranar Laraba.
Binciken jaridar Daily Trust ya gano cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai bayyana Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojojin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a yi wa rundunar soji garanbawul
Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Bola Tinubu zai sanar da sabon babban hafsan sojin kasar nan bayan majalisa ta amince da nadin Laftanar Janar Olufemi Oluyede.
Wannan na nufin dole ne yi sauye-sauye a rundunar, inda aka samu rahoton cewa za a mayar da wasu daga cikin tsarorin Olufemi Oluyede zuwa hedikwatar tsaro.
Za a tilastawa manyan sojoji yin ritaya?
Wani babban sojan kasar nan da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana cewa ba za a tilastawa sojojin 39 yin ritaya ba saboda nadin sabon babban hafsan soja.
Ya bayyana cewa sai dai za a iya sauyawa wasu daga manyan Janar din wurin aiki, amma za su cigaba da aikinsu a rundunar sojin Najeriya.
Tinubu ya shiga jimamin rasuwar hafsan sojoji
A baya mun ruwaito cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya shiga jimamin rauswar babban hafsan sojiojin kasar nan, inda ya bayar da umarnin kasa ta shiga makoki ta hanyar sauke tutoci.
Sanarwar da hadimin Tinubu, Bayo Onanuga ya ftar ta bayyana cewa shugaban kasar ya dage taron majalisar zartarwa ranar Laraba bayan rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a daren Talata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng