Yadda 'Yan Bindiga Suka Kakaba Harajin N150m kan Mutanen Kauyukan Zamfara

Yadda 'Yan Bindiga Suka Kakaba Harajin N150m kan Mutanen Kauyukan Zamfara

  • Tsagerun ƴan bindiga na ci gaba da takurawa mutanen ƙauyukan jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Ƴan bindigan sun ƙaƙaba harajin N150m kan wasu ƙauyukan da ke yammacin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar
  • Gwamnatin Zamfara ba ta da masaniya kan harajin amma ba za ta bari ƴan bindiga su raba mutane da kuɗinsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun ƙaƙaba harajin N150m kan wasu ƙauyukan jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun yanka harajin da kowane ƙauye zai biya wanda ya kama daga N7m zuwa N20m.

'Yan bindiga sun sanya haraji a Zamfara
'Yan bindiga sun sanya harajin N150m a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan bindiga sun ƙaƙaba haraji a Zamfara

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wata majiya ce ta shaida mata hakan.

Kara karanta wannan

Fadan daba ya jawo sanadiyyar rasa rayukan mutane a Benue

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne yayin da ake jimamin sace sama da mutane 100 da ƴan bindiga suka yi a jihar.

Majiyar ta bayyana cewa shugaban ƴan bindigan da ya maye gurbin, Kachalla Sububu, Kachalla Mati, ya sanya harajin N50m ga mutanen ƙauyen Kewaye sannan ya ba su wa'adin sati biyu da su biya.

"Shugaban ƴan bindiga Dan Yusuf wanda ƙanin Ado Aleiro ne, ya sanya harajin sama da N100m wanda ya rarraba tsakanin ƙauyukan da ke yammacin ƙaramar hukumar Tsafe."
"Mutanen ƙauyukan Kucheri za su biya N20m, Kwalfada, N7m, Magazawa, N7m, Barebari, N7m, Bilbis, N20m, Danjibga, N20m, Keita, N20m da Kunchin Kalgo, N20m."

- Wata majiya

Me gwamnati ta ce kan harajin yan bindigan

Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, Bala Muhammad Mairiga, ya bayyana cewa gwamnati ba ta samu ƙorafi ba daga mutanen ƙauyukan kan batun harajin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi kokarin da Tinubu ke yi domin rage tsadar rayuwa a Najeriya

"Dangane da batun haraji, magana ta gaskiya ba mu samu wani ƙorafi ba daga ƙauyukan da lamarin ya shafa. Amma duk da haka za mu yi bincike domin ganin abin da za mu iya yi a kai."
Gwamnatin jihar Zamfara ba za ta zura ido ta bari ƴan bindiga su ƙwacewa mutane kuɗinsu ba.
Gwamnati ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal na yin bakin ƙoƙarinta wajen magance ayyukan ƴan bindiga kuma za ta ci gaba da yin duk abin da za ta iya yi domin kawo ƙarshen matsalar."

- Bala Muhammad Mairiga

Rundunar tsaro ta gargaɗi ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin ƙasar nan ta jaddada matsayarta na kai farmaki har maboyar yan ta'addan da su ka addabi jama'a, musamman a Arewacin ƙasar nan.

Shugaban rundunar Fansar Yamma, Manjo Janar Oluyinka Soyele ne ya yi gargadin jim kadan bayan ganawarsa da Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng