An Samu Karin Bayani kan Yan Ta'addar Lakurawa da Suka Shigo Arewa

An Samu Karin Bayani kan Yan Ta'addar Lakurawa da Suka Shigo Arewa

  • Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Sokoto ta yi bayani kan wata sabuwar kungiyar yan ta'adda da ta bullo mai suna Lakurawa
  • Kakakin yan sandan jihar, ASP Ahmed Rufa'i ya tabbatar da cewa yan kungiyar Lakurawa sun yadu a kananan hukumomi Sokoto biyar
  • ASP Ahmed Rufa'i ya kara da cewa a wasu lokutan ana samun miyagun suna yin fada da yan bindiga masu garkuwa da mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Jihar Sokoto - An kara samun bayanai kan kungiyar yan ta'addar Lakurawa da suka ɓullo a Sokoto.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa akwai yan ta'addar a wasu kananan hukumomin jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun gwabza faɗa da yan bindiga, an kashe wasu miyagu

Yan sanda
Yan sanda sun yi karin haske game da Lakurawa. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kakakin yan sanda jihar, ASP Rufa'i Ahmed ne ya tabbatar da samuwar yan ta'addar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai Lakurawa inji yan yan sanda

Biyo bayan maganganu da aka rika yi a kan sabuwar kungiyar yan ta'addan Lakurawa, rundunar yan sanda ta tabbatar da samuwarsu.

Kakakin yan sanda, ASP Ahmed Rufa'i ya tabbatar da cewa yan ta'addar suna zaune ne a kananan hukumomi biyar na jihar Sokoto.

Lakurawa sun daɗe a jihar Sokoto

ASP Ahmed Rufa'i ya bayyana cewa yan ta'addar Lakurawa sun dade suna zaune a yankunan Sokoto kuma suna dauke da manyan makamai.

Rundunar yan sanda ta kara da cewa yan ta'addar Lakurawa na kokarin tilasta mutane bin tsarin fahimtar addini da suka zo da ita.

The Cable ta ruwaito cewa daga cikin ƙananan hukumomin da miyagun suke akwai Gudu, Tangaza, Binji da Ilela.

Kara karanta wannan

Sabuwar kungiyar yan ta'adda na raba miliyoyi domin rudar matasan Arewa

Lakurawa na fada da yan bindiga

ASP Ahmed Rufa'i ya tabbatar da cewa a wasu lokuta yan ta'addar Lakurawa na yakar masu garkuwa da mutane.

Lakurawa na fada da masu garkuwa da mutane ne a bisa cewa suna ta'addanci kan al'umma.

Lakurawa na ba matasa kudi har N1m

A wani rahoton, kun ji cewa yan ta'addar Lakurawa na amfani da kudi wajen rudan matasa domin shiga tafiyarsu.

Rahotanni sun tabbatar cewa yan ta'addar Lakurawa na ba duk matashin da ya shiga tafiyarsu kudi har Naira miliyan aya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng