Hadimar Gwamna Abba kuma Jarumar Kannywood Ta Fice daga NNPP zuwa APC

Hadimar Gwamna Abba kuma Jarumar Kannywood Ta Fice daga NNPP zuwa APC

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rasa ɗaya daga cikin masu taimaka masa bayan ta fice daga jam'iyyar NNPP da Kwankwasiyya
  • Jarumar Kannywood, Asma'u Abdullahi ta tsallaka zuwa jam'iyyar APC mai adawa a jihar bayan ta yi murabus daga muƙaminta a Kano
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin, wanda ya sanar da shigowarta APC ya buƙaci ta zama jakada ta gari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jarumar Kannywood kuma mai taimakawa gwamnan Kano, Asma'i Abdullahi, ta fice daga jam'iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya.

Asma'u Abdullahi bayan ficewarta daga NNPP ta koma jam'iyyar APC mai adawa a jihar.

Jarumar Kannywood ta koma APC a Kano
Asma'u Abdullahi ta koma APC Hoto: @barauijibrin
Asali: Twitter

Jarumar Kannywood ta bar NNPP zuwa APC

Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da shigowarta cikin jam'iyyar APC a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

NNPP a Kano: Kusoshin jam'iyya sun fara nuna shakku kan shugabancin Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa Asma'u Abdullahi ta sanar da ficewarta daga jam'iyyar NNPP ne a yayin wata ziyara da ta kai masa a Abuja.

Sanata Barau Jibrin ya kuma bayyana cewa Asma'u Abdullahi ta yi murabus daga muƙaminta ta hadimar Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan barin NNPP da tafiyar Kwankwasiyya.

"Na karbi fitacciyar jarumar Kannywood kuma mai taimakawa gwamnan jihar Kano, Asma'u Abdullahi Wakili daga jam'iyyar NNPP zuwa APC."
"Yayin da na ke maraba da ita, na nanata ƙudurinmu na ganin mun yi wa dukkanin ƴan jam’iyyar adalci."
"A matsayinta na jarumar masana’antar nishadantarwa, na buƙace ta da ta yi aiki tuƙuru, ta kuma kasance jakada ta gari ta masana’antar, jam’iyyarmu da ma ɗaukacin Arewacin Najeriya."
"Muna yi mata maraba."

- Sanata Barau Jibrin

Gwamna Abba ya fusata kan batun 'tsaya da ƙafarka'

Kara karanta wannan

"Kwankwaso ba zai yafewa Abba laifuka 3 ba:" Madakin Gini ya fara tone tone

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana shirin ɓallewa daga gidan jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

Gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa taken da ake yaɗawa na, 'Abba tsaya da ƙafarka" babban cin mutunci ne a gare shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng