"Mun Sha Wahala": Yaran da Aka Tsare Sun Bayyana Azabar da Aka ba Su
- Yaran da aka tsare saboda zargin shiga zanga-zanga sun samu ƴanci bayan shugaba Bola Tinubu ya yi musu afuwa
- Wasu daga cikinsu sun bayyana irin baƙar azaba da wahalar da suka sha a kwanakin da suka yi a hannun hukuma
- Yaran sun bayyana cewa abinci yana yi musu wahalar samu sannan an ajiye su wuri ɗaya tare da ruƙaƙƙun masu laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ƴara da dama da aka cafke saboda zanga-zanga sun bayyana irin wahalar da suka sha lokacin da aka tsare su.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi musu afuwa bayan sun kwashe kwanaki masu yawa a tsare.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa wasu daga cikinsu sun shaida mata irin azabar da suka sha lokacin da aka tsare su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaran dai bayan an dawo da su Kano, an kai su asibitin ƙwararru na Muhammadu Buhari domin kula da lafiyarsu.
Yaran da aka tsare na kwanaki babu abinci
Ɗaya daga cikinsu mai suna Umar Ali mai shekara 15 ya bayyana cewa a wasu lokutan sai su yi kwanaki uku ba tare da an ba su abinci ba.
"Mun sha azaba, mun wahala sosai. Wasu lokutan muna yin kwanaki uku ba tare da abinci ba. Sannan ko da an ba mu abinci bai isar mu."
- Umar Ali
Umar Ali ya musanta shiga zanga-zangar ya ce an cafke shi ne a Kwana Hudu cikin ƙaramar hukumar Ungogo, lokacin da yake hanyar zuwa kasuwa domin yin aikin da zai samu kuɗi.
Ya ƙara da cewa lokacin da suke tsare an ajiye su a cikin duhu wanda hakan ya sanya wasu daga cikinsu suka samu matsala a kotu lokacin da aka gurfanar da su.
An haɗa yaran da riƙaƙƙun masu laifi
Wani ƙaramin yaro mai suna Ibrahim Aliyu Musa, wanda aka kai shi Abuja daga Kano kwana ɗaya bayan an cafke shi, ya ce da shi da wasu, an ajiye su wuri ɗaya tare da riƙaƙƙun masu laifi.
"Ina daga cikin waɗanda aka ajiye wuri ɗaya tare da riƙaƙƙun masu laifi. Wasu lokutan muna shafe kwanaki ba tare da mun samu abinci ba."
"Abincin ba wani na kirki ba ne, ya yi kaɗan kuma ko ɗanɗano bai da shi. Suna ba mu wake da safe, shinkafa da rana sannan da daddare a ba mu gabza."
- Ibrahim Aliyu Musa
Haka kuma, wani yaro mai shekara 13 ya bayyana cewa an cafke shi ne a Gadon Kaya cikin ƙaramar hukumar Gwale, bisa zargin ɗaga tutar Rasha, laifin da ya musanta aikatawa.
"An cafke ni ne a ranar, 15 ga watan Agusta sannan aka tafi da ni Abuja washegari. An ajiye mu a Abattoir SARS a Abuja.
"Waje ɗaya aka sanya mu tare da riƙaƙƙun masu aikata laifuka a iya kwanakin da muka yi."
- Wani yaro
Gwamna Abba ya ja kunnen yaran da aka tsare
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ja kunnen kananan yara a kan batun zanga zanga da za a iya gudanarwa a nan gaba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hori yaran da gwamnatin tarayya ta daina shari’a da su da kar su kara shiga wata zanga zanga a nan gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng