Gwamna Ya Faranta Ran Ma'aikata, Ya Amince da Mafi Karancin Albashin N80,000

Gwamna Ya Faranta Ran Ma'aikata, Ya Amince da Mafi Karancin Albashin N80,000

  • Gwamnatin Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde, ta faranta ran ma'aikatan jihar ta hanyar amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi
  • Gwamna Seyi Makinde ya amince da N80,000 a matsayin ƙarancin albashin da zai biya ma'aikata gwamnati a jihar
  • Amincewar da gwamnan ya yi ta biyo bayan kammala aikin da kwamitin da aka kafa kan mafi ƙarancin albashin ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Gwamnatin Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.

Gwamna Seyi Makinde ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin N80,000 wanda za a riƙa biyan ma’aikatan jihar.

Gwamna Makinde ya amince da mafi karancin albashi
Gwamnan Oyo ya amince da sabon mafi karancin albashi Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Makinde ya amince da mafi ƙarancin albashi

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, Prince Dotun Oyelade, ya bayyana hakan wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Karancin abinci: Abubuwan da suka jefa mutane cikin yunwa da mafitarsu a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ne ya ba da shawarar hakan kuma ya samu amincewar gwamna Seyi Makinde domin aiwatar da sabon tsarin albashin.

Ya ƙara da cewa za a fara aiwatar da sabon tsarin ne da zarar kwamitin ya kammala gyare-gyaren da yake yi, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Gwamna Makinde na gatanta ma'aikata a Oyo

Kwamishinan ya bayyana cewa jihar na biyan albashin ma’aikata ne a ranar 25 ga kowane wata tun lokacin da Gwamna Makinde ya hau mulki a shekarar 2019.

Ya kuma ce gwamnan ya fara biyan tsohon mafi ƙarancin albashi na N30,000 ana amincewa da shi shekara huɗu da suka gabata.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnan yana biyan ƴan fansho da kuɗaɗen giratuti ba tare da jinkiri ba.

Zulum ya fara biyan albashin N70,000

Kara karanta wannan

Ana murna gwamna a Arewa ya fara biyan ma'aikata sabon albashi na N70,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umaru Zulum.ta tabbatar da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi.

Shugaban kwamitin da aka kafa kan mafi ƙarancin albashin, Dokta Babagana Mallambe, ya ce tuni ma'aikata suka fara ganin sabon albashin a asusun bankunansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng