Tinubu Ya Shirya Gwangwaje Ƙananan Yan Kasuwa, Ya Fadi Ka'idojin Cin Gajiyar N75bn
- Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin ba da bashi ga kananan yan kasuwa domin bunkasa tattalin arziki
- Gwamnatin Bola Tinubu ta fitar da ka'idojin cin gajiyar basukan N75bn domin bunkasa harkokin kasuwancinsu
- Shugaban bankin kasuwanci a jihar Akwa Ibom ya tabbatar da haka yayin kaddamar da shirin domin yan kasuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Akwa Ibom - Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan shirin ba da basuka har N75bn ga kananan yan kasuwa a Najeriya.
Gwamnatin Bola Tinubu ta fadi ka'idojin da masu cin gajiyar za su cike kafin samun basukan domin inganta kasuwanci.
Shirin ba yan kasuwa bashin N75bn ya kankama
Manajan bankin kasuwanci (BOI) a jihar Akwa Ibom, Tolulope Toluwase shi ya bayyana haka a birnin Uyo, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Toluwase ya fadi haka yayin kaddamar da shirin a birnin Uyo inda ya jero yadda ka'idojin suke.
Ya ce shirin zai samar da ayyuka ga ƙananan yan kasuwa 75,000 inda zai samar da aiki kai tsaye ga mutane 75,000.
Har ila yau, Toluwase ya ce shirin zai kuma samar wasu ayyuka ba kai tsaye ba akalla ga mutane 150,000 a Najeriya.
Ka'idojin da mutum zai cike kafin samun bashin
Daga cikin ka'idojin ya ce mutum zai kawo mai tsaya masa ma'aikaci a Gwamnatin Tarayya da ke mataki na 10.
Sannan zai kawo hotunan ma'aikacin guda hudu da na shi da kuma lambobin BVN da NIN da kuma shaidan katin aiki.
Ya ce duk wanda ya yi nasarar cike ka'ida zai samu bashin N1m domin inganta harkokin kasuwancinsa.
Tinubu zai ba gidaje miliyan 3 tallafi
Kun ji cewa yayin da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya, shugaba Bola Tinubu ya amince da kawo sauki ga iyalai miliyan uku a kasar.
Tinubu ya amince da ba da N50,000 ga iyalai a duka shiyyoyin kasar har na tsawon watanni uku domin rage musu radadi
Hakan na zuwa ne yayin da al'ummar Najeriya ke cikin mummunan yanayi tun bayan cire tallafin man fetur da ka yi a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng