Pantami Ya Yi Alhinin Rasuwar Janar Taoreed Lagbaja, Ya Yi Masa Addu'a

Pantami Ya Yi Alhinin Rasuwar Janar Taoreed Lagbaja, Ya Yi Masa Addu'a

  • Farfesa Isa Ibrahim Pantami ya yi alhinin rashin da aka yi na babban hafsan sojojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja
  • Tsohon ministan na sadarwa ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya ba da gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya a Najeriya
  • Malamin ya yi wa iyalansa, gwamnatin tarayya da rundunar sojojin Najeriya ta'aziyya game da wannan babban rashin da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi alhinin rasuwar hafsan sojojin ƙasan Najeriya (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

A ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamban 2024 gwamnatin tarayya ta sanar da rasuwar Taoreed Lagbaja bayan ya yi ƴar gajeruwar jinya.

Kara karanta wannan

Uwargidar shugaban ƙasa da wasu mata 2 sun dura gidan marigayi hafsan sojin ƙasa

Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar Lagbaja
Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar Taoreed Lagbaja Hoto: @HQNigerianArmy, @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

Me Isa Pantami ya ce a kan rasuwar Lagbaja?

Farfesa Pantami ya yi ta'aziyyar marigayin a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya yaba da irin gudunmawar da marigayin ya ba da wajen wanzar da zaman lafiya.

Ya yi wa iyalansa, rundunar sojojin Najeriya, gwamnatin tarayya da sauran hukumomin tsaro ta'aziyyar wannan gagarumin rashi da aka yi.

Farfesa Pantami ya yi ta'aziyyar Lagbaja

"Na yi baƙin ciki da jin labarin rasuwar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya, bayan ya yi rashin lafiya."
"Za mu ci gaba da yabawa da irin gudunmawar da ya bayar wajen kare ƙasarmu, tun daga farkon aikinsa har zuwa rasuwarsa, wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali."
"Ina miƙa saƙon ta'aziyyata ga iyalansa, ƴan uwa, rundunar sojojin Najeriya, sauran hukumomin tsaro, da gwamnatin Najeriya."

Kara karanta wannan

'Jarumi ne': Buhari ya jajanta mutuwar Lagbaja, ya fadi farkon ganinsa a gidan soja

"Allah gafarta masa kurakuransa, shigar da shi Aljannah tare da waɗanda suka rasu."

- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami

Uwargidan Tinubu ta je ta'aziyyar Lagbaja

A wani labarin kuma, kun.ji cewa uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi babban hafsan sojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Oluremi Tinubu ta kai wannan ziyara ne tare da ita akwai matar mataimakin shugaban ƙasa, Hajia Nana Shettima, da matar mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng