'Jarumi ne': Buhari Ya Jajanta Mutuwar Lagbaja, Ya Fadi Farkon Ganinsa a Gidan Soja
- Bayan mutuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja, tsohon shugaban kasa ya janatawa yan Najeriya kan rashin da aka yi
- Muhammadu Buhari ya kadu da mutuwar Taoreed Lagbaja inda ya ce tabbas an yi babban rashi a kasar Najeriya baki daya
- Buhari ya bayyana irin gudunmawar da Lagbaja ya bayar da yadda ya dauki hankalinsa a lokacin da yake mulkin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajanta kan mutuwar hafsan sojoji.
Buhari ya kadu da rasuwar Laftanar-janar Taoreed Lagbaja inda ya ce an yi rashin hazikin soja da ya mayar da hankali wurin bautawa kasa.
"Mun yi rashin jarumi": Buhari kan mutuwar Lagbaja
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon hadiminsa, Bashir Ahmad ya wallafa a shafin X a yau Laraba 6 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Buhari ya ce Najeriya ta yi rashin jajirtaccen soja wanda ya bautawa kasar cikin jarumta.
Tsohon shugaban kasar ya ce ya fara sanin Lagbaja ne lokacin da yake mulki shi kuma yana rike da mukamin kwamandan sojoji.
Buhari ya ce Lagbaja ya dauki hankalinsa a lokacin duba da yadda ya rike aikinsa da muhimmanci da kuma nuna kulawa a tsaron kasa.
Buhari ya magantu kan haduwarsa da Lagbaja
"Lokacin da nake mulkin Najeriya, Lagbaja a lokacin yana kwamandan sojoji ya dauki hankali na saboda jajircewarsa."
"Lagbaja ya ba da gudunmawa sosai a tsaron Najeriya musamman a Zaki da ke Benue da 'Operation Lafiya Dole a Borno."
"Sauran sun hada da 'Operation Forest Sanity a Kaduna da Niger da Udoka a Kudu maso Gabas."
- Muhammadu Buhari
Buhari daga bisani ya yi addu'a ga mamacin da ba iyalansa hakuri tare da rokon Allah ya biya shi sadaukarwar da ya yi.
Ministan tsaro ya jajantawa mutuwar Lagbaja
Kun ji cewa Ministocin tsaro, Badaru Abubakar da Bello Matawalle sun jajanta kan mutuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja.
Ministocin sun kadu da rasuwar Laftanar-janar Taoreed Lagbaja inda suka jajantawa Bola Tinubu kan babban rashin da aka yi.
Asali: Legit.ng