Yan Bindiga Sun Sace Limami da Mutane sama da 100 a Zamfara
- Rahotanni da suka fito daga jihar Zamfara na nuni da cewa yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi ta'asa a kusa da Gusau
- Mazauna yankin sun tabbatar da cewa yan bindigar sun sace mutane sama da 100 a cikinsu har da mata da kananan yara da dama
- A cikin mutanen da aka sace akwai limamin garin wanda aka bayyana cewa a lokacin da aka sace shi yana fama da rashin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Rahotanni da suka fito daga jihar Zamfara na nuni da cewa yan bindiga sun kai hari yankin Wanke.
A yayin kai harin, yan bindigar sun sace mutane sama da 100 kuma sun kora su daji kamar shanu.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa cikin wanda bada miyagun suka sace akwai mata da yara kanana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sace mutane sama da 100 a Zamfara
Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kai hari yankin Wanke inda suka sace mutane sama da 100.
Wani wanda ya tsallake rijiya ta baya ya bayyana cewa yan bindigar sun sace mutane fiye da 50 unguwar Sabon Layi.
Biyo bayan haka yan bindigar suka matsa unguwar Dogon Hayi suka yi gaba da mutane kimanin 50.
Yadda aka dauke mutane 100 a jihar Zamfara
Mutane garin sun bayyana cewa yan bindigar sun bi gida gida suna tattaro mata, yayin da suka kama wasu suna ƙoƙarin guduwa.
Haka zalika yan bindigar sun bi mutane a kan babura suka kama su daga nan kuma suka tafi da su cikin daji.
Zamfara: 'Yan bindiga sun sace har da limami
Rahotanni sun tabbatar da cewa cikin mutanen da aka sace akwai limamin Wanke wanda yana fama da ciwon kafa.
Mutanen garin sun bayyana cewa sau biyu ana sace limamin garin kuma ciwon da yake fama da shi ma yan bindiga ne suka masa rauni.
An kashe yan bindiga a Delta
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sanda ta gwabza fada da wasu yan bindiga masu garkuwa da mutane a Delta.
Rahotanni sun nuna cewa miyagun ne suka fara bude wuta kan yan sanda wanda daga bisani aka kashe yan bindiga biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng