Yan sanda Sun Gwabza Faɗa da Yan Bindiga, An Kashe Wasu Miyagu
- Rundunar yan sanda a jihar Delta ta yi wani kazamin fada da wasu miyagu yan bindiga da suka fitini al'umma a yankin Warri
- Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar ne suka fara yi wa yan sanda kwanton ɓauna a wani samame da jami'an tsaron suka fita
- Jami'an yan sanda sun yi nasarar kwato makaman da yan bindigar ke amfani da su wajen kai hare hare kan al'umma a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - Rundunar yan sanda a jihar Delta ta samu nasara kan gungun wasu miyagu yan bindiga.
Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun yi musayar wuta da yan bindigar yayin da miyagun suka afkawa jami'an tsaro.
Jaridar Punch ta wallafa cewa kakakin yan sandan jihar Delta, SP Bright Edafe ya tabbatar da kashe yan bindigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda sun gwabza da yan bindiga
Rundunar yan sanda a ƙaramar hukumar Ighelli ta fita wani samame na musamman domin neman wasu yan bindiga.
Yayin da yan sandan suke farautar miyagun, yan bindigar suka yi kwanton ɓauna suka fara bude wuta.
Daga nan yan sanda suka fara sakin wuta kan yan bindigar kuma suka samu nasarar hallaka biyu sauran suka tsere.
An kashe yan bindigar da suka fitini Warri
Vanguard ta wallafa cewa kakakin yan sanda, SP Bright Edafe ya ce bincike ya tabbatar da cewa yan bindigar ne suka fitini mutane a kan hanyar Warri zuwa Sapele.
Haka zalika SP Bright Edafe ya kara da cewa suna kai hare hare a yankin Mosogar, Oghara da Ighelli.
Makaman yan bindiga da aka kwato
Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa ta kwato bindiga ƙirar Pistol cike da harsashi wajen miyagun.
Dadin dadawa, jami'an tsaron sun kwato bindiga ƙirar AK-47 da aka loda mata harsashi bayan sun hallaka yan ta'addar.
Yan bindiga sun fitini mutane a Edo
A wani rahoton, kun ji cewa mutanen ƙaramar hukumar Etsako ta Gabas a jihar Edo sun koka kan fitinar yan bindiga.
Shugabar karamar hukumar, Benedicta Attoh ta bukaci gwamnatin tarayya ta kawo musu dauki domin kisan mutane ya yawaita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng