Taoreed Lagbaja: Cikakkken Jerin Hafsoshin Sojojin Kasa da Suka Rasu a Ofis
- A ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba aka tashi da labarin rasuwar hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja
- Marigayin ba shi ba ne hafsan sojojin Najeriya da ya rasu a lokacin da yake riƙe da muƙamin na shugaban dakarun tsaron ba
- Kafin Lagbaja akwai hafsoshin sojojin ƙasan Najeriya biyu da suka rasu suka rasu a kan muƙamin ciki har da Attahiru Ibrahim
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi Read
Najeriya na cikin alhinin rasuwar babban hafsan sojojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya rasu ranar Talata a Legas bayan gajeruwar rashin lafiya.
Rasuwar Taoreed Lagbaja ta zo ne ƙasa da shekara ɗaya bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa shi a muƙamin.
Hafsoshin sojojin ƙasa da suka rasu a ofis
Rasuwar Lagbaja kuma ita ce karo na uku da wani babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya ya rasu yana kan muƙamin, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin tsofaffin hafsoshin sojan ƙasa (COAS) da suka rasu a ofis:
Joseph Akahan (Agusta 1967)
An naɗa Joseph Akahan mai shekara 30 a matsayin babban hafsan sojojin ƙasa, jim kaɗan kafin ɓarkewar yaƙin basasar Najeriya a shekarar 1967.
Jaridar The Nation ta ce bayan ya ziyarci dakarun sojoji a Nsukka, ya koma garinsa na Gboko domin ya ɗan samu hutu.
Yayin da yake hanyar komawa Makurdi, jirgi mai saukar ungulu da ke ɗauke da shi ya yi hatsari, inda ya yi sanadiyyar mutuwarsa tare da wasu matuƙan jirgin guda biyu.
Attahiru Ibrahim (Mayu 21, 2021)
Laftanar Janar Attahiru Ibrahim, wanda aka naɗa a watan Janairun 2021 domin maye gurbin Tukur Buratai, ya rasu ne watanni kaɗan bayan ya fara wa'adinsa.
Attahiru Ibrahim ya rasu bayan jirgin da ke ɗauke da shi ya yi hatsari, wanda ya yi sanadiyyar rasuwarsa da wasu mutane 10 da ke tare da shi.
Taoreed Lagbaja (Nuwamba 5, 2024)
Taoreed Lagbaja wanda tsohon ɗalibi ne a kwalejin yaƙi ta sojojin Amurka, ya fara aiki da rundunar sojojin Najeriya a shekarar 1992.
Kafin a naɗa shi COAS a ranar 19 ga watan Yuni, 2023, ya yi aiki a matsayin kwamandan runduna a bataliya ta 93 da kuma bataliya ta musamman ta 72.
Ya taka muhimmiyar rawa a ayyukan tsaro na cikin gida da dama, ciki har da Operation ZAKI a jihar Benue, Lafiya Dole a Borno, Udoka a Kudu maso Gabashin Najeriya, da kuma Operation Forest Sanity a jihohin Kaduna da Neja.
Rasuwar Lagbaja: Tinubu ya ɗage taron FEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, babban kwamandan sojojin kasar nan, ya bayar da umarnin dage taron majalisar zartaswa ta tarayya.
Shugaban ƙasan ya dage taron majalisar zartarwar ne sakamakon rasuwar babban hafsan sojojin kasan Najeriya, Taoreed Lagbaja.
Asali: Legit.ng